Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja Afrika
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe Afrika
  • Billiri/Balanga: Kotu Ta Bayar Da Umarnin Sabon Zabe, Amma Gwamnati Ta Yi Shiru – AB Ibrahim Afrika
  • Hukumomin Kashe Gobara A Gombe Sun Ƙarfafa Haɗin Kai Don Hana Gobara A Lokacin Bazara Labarai

RUWASSA Ta Raba Magunguna Kyauta A Cibiyoyin Lafiya Dake Gombe
Published: October 18, 2026 at 4:23 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar Samar da Ruwa da Tsaftar Muhalli a Ƙauyuka ta jihar Gombe (RUWASSA) ta raba magunguna da kayan aikin lafiya ga wasu cibiyoyin kula da lafiya a ƙananan hukumomi uku na jihar, a wani yunƙuri na inganta ayyukan kiwon lafiya da sauƙaƙa wa al’umma samun muhimman magunguna.

Cibiyoyin da suka amfana da tallafin sun haɗa da Cibiyar Kula da Lafiya ta Farko (PHCC) ta Garko da ke Ƙaramar Hukumar Akko, Cibiyar Kula da Lafiya ta Farko ta Bangu da ke Ƙaramar Hukumar Balanga, da kuma Cibiyar Kula da Lafiya ta Farko ta Gombe Abba da ke Ƙaramar Hukumar Dukku.

Babban Manajan Hukumar kuma Mai Kula da Ayyukan, Injiniya Muhammad Ahmad Gibirimu, ya samu wakilcin Jami’in Gudanarwa na hukumar, Adamu Buji, wanda ya jagoranci aikin rabon magungunan a madadinsa.

Ana sa ran tallafin zai taimaka wa ma’aikatan lafiya wajen kula da marasa lafiya, tare da inganta samun muhimman magunguna a cibiyoyin da suka amfana.

A Ƙaramar Hukumar Balanga kuwa, shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Salisu Ibrahim, ya tarbi tawagar hukumar a ofishinsa, inda ya tabbatar musu da cewa za a sanya ido kan yadda ake rabawa da amfani da magungunan ta hannun mai kula da cibiyoyin lafiya na ƙaramar hukumar, Mista Danjuma K. Mauni.

Daga nan ne tawagar ta zarce zuwa cibiyar lafiyar Bangu, inda jami’in da ke kula da cibiyar, Mista David Seidu Jatau, ya tarbe su.

Shugaban gundumar Bangu, Alhaji Danjuma Sulaiman, wanda Malam Aliyu Gwadabe ya wakilta, ya bayyana farin cikinsa kan tallafin, tare da alƙawarin tabbatar da an yi amfani da magungunan yadda ya kamata, musamman wajen taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi a cikin al’umma.

Rabon magungunan ga cibiyoyin lafiya na Garko a Akko, Bangu a Balanga da Gombe Abba a Dukku ya nuna muhimmancin ci gaba da tallafin gwamnati da haɗin gwiwa wajen ƙarfafa ayyukan kiwon lafiya a matakin al’umma.

Hukumar RUWASSA ta jaddada aniyarta ta ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen da za su inganta lafiyar al’umma da kuma kyautata rayuwar mazauna Jihar Gombe.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Buni Ya Amince Da Sabon Tsarin Albashin Ma’aikatan Jihar Yobe
Next Post: Rundunar ’Yan Sandan Bauchi Ta Yi Gargaɗi Kan Ɗaukar Doka A Hannu Bayan Kama Mutum 17

Karin Labarai Masu Alaka

UNICEF Ta Tallafawa Jihar Bauchi Da Babura Afrika
Fadar Shugaban Kasa Ta Karyata Jita-Jitar Yunkurin Sanya Wa Tinubu Guba A Abinci Afrika
Amurka Ta Jefa Makamin Tomahawk A Makarantar Yara Mata Afrika
Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai Afrika
Kasar Israela Zata Gina Sansani A Gaza Afrika
An Gano Gawar Dan Yawon Bude Ido A Kasar Chadi Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Agadez: An Gudanar Da Jana’izar Mutane Da Suka Mutu A Wani Harin Ta’addanci
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja
  • Tambuwal Ya Karyata Rahotannin Shirin Komawarsa APC
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Za’ayi Jana’izar Marigayi Ali Khamenei a Tehran, Qom da Mashhad Afrika
  • Ambaliyar Ruwa Ya Tilastawa Dubban Jama’a Rasa Muhallensu A Morocco Afrika
  • Kasar Jamus Ta Haramtawa Yara Kasa Da Shekaru 14 Hawa Dandalin Sada Zumunta Labarai
  • Sojojin Kasar Uganda Sun Bazama Neman Bobi Wine Sakamakon Rikicin Bayan Zabe Siyasa
  • Zargin Tauye Ka’idojin Zabe: Malam Pantami Ya Janye Daga Takara Afrika
  • Adamu: “Yakar Cin Hanci Daga Tushe Itace Mafita Daya Tilo” Labarai
  • Anyi Asarar Biliyoyin Naira A Gobarar Kasuwar Singa Labarai
  • Bayan Ya Ziyarci Kwankwaso Gawuna Zai Karbi Katin ADC Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.