Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja Afrika
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe Afrika
  • Billiri/Balanga: Kotu Ta Bayar Da Umarnin Sabon Zabe, Amma Gwamnati Ta Yi Shiru – AB Ibrahim Afrika
  • Hukumomin Kashe Gobara A Gombe Sun Ƙarfafa Haɗin Kai Don Hana Gobara A Lokacin Bazara Labarai

Tambuwal Ya Karyata Rahotannin Shirin Komawarsa APC
Published: October 20, 2026 at 4:26 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Sanata Tambuwal na nan daram da cikakken goyon bayansa ga jam’iyyar ADC. Hankalinsa ya karkata ne wajen ƙarfafa jam’iyyar, gina haɗin gwiwa mai faɗi da kuma wayar da kan ’yan Najeriya gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Sanarwar Prince Daniel Mai Bai wa Sanata Aminu Waziri Tambuwal Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa ya sanar da cewa, a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke neman amsoshi kan manyan ƙalubalen tattalin arziki, tsaro da shugabanci, ya kamata tattaunawar jama’a ta mayar da hankali kan muhimman batutuwa da gaskiya.

Hasashe marar tushe bai kamata ya ɗauke hankali daga muhimmin aikin samar wa ’yan Najeriya ingantaccen shugabanci da kyakkyawar makoma ba.

Muna kira ga magoya baya da sauran jama’a da su mayar da hankali kan ayyukan da ke gabansu. Ƙudurin Sanata Tambuwal na tabbatar da shugabanci mai ɗaukar alhaki, kiyaye ƙa’idojin dimokuraɗiyya da kuma inganta rayuwar ’yan Najeriya bai sauya ba.

Muna kira ga kafafen yaɗa labarai da masu sharhi a kafafen sada zumunta da su tabbatar da sahihancin irin waɗannan bayanai ta hanyar tuntuɓar Ofishin Yaɗa Labarai na AWT kafin wallafa su. Bai kamata a gabatar da hasashe a matsayin tabbatacciyar gaskiya ba.

Afrika, Labarai, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe
Next Post: Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja

Karin Labarai Masu Alaka

Jami’an Diflomasiyyar Iran Dana Amurka Sun Tattauna A Kasar Oman Afrika
Jihar Gombe Ta Saka Hannu Kan Yarjejeniya Da Kamfanonin Tunisiya Kimiya
Gombe Ta Yi Fice A Duniya: Maryam Dan’azumi Ta Lashe Gasar Alƙur’ani Na Ƙasa Da Ƙasa Afrika
Ana Kokarin Kawo Karshen Matsalar Kashe Matafiya A Filato Afrika
Gwamnatin Najeriya Ta Fara Aikin Babbar Hanyar Da Za Ta Haɗa Jihohin Arewa Afrika
Shugaban Lebanon Ya Nemi Gudanar Da Shawarwari Kai Tsaye Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Agadez: An Gudanar Da Jana’izar Mutane Da Suka Mutu A Wani Harin Ta’addanci
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja
  • Tambuwal Ya Karyata Rahotannin Shirin Komawarsa APC
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Asusun IMF Zai Bawa Kasar Misra Lamunin Sama Da Dala Biliyan 2 Sauran Duniya
  • CHAN Ta Duba Lafiyar Idanun ‘Yan Jarida A Filato Afrika
  • Shugaban Lebanon Ya Nemi Gudanar Da Shawarwari Kai Tsaye Afrika
  • ‘Yan-Ta’adda Sun Yi Ma Wasu Mutane Yankan Rago A Jihar Neja Labarai
  • Kocin Ranchers Bees Ya Yi Murabus Wasanni
  • Guterres: Babban Kuskure Ne Yadda Isra’ila Ta Kai Farmaki A Gaza Labarai
  • Motar Kungiyar Kwallon Kafar Bayelsa United Ta Yi Hatsari Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Sojoji Sun Murkushe ‘Yan Bindiga A Jihar Sakkwato Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.