Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Tinubu Zai Ciwo Bashin Dala Biliyan 7.7 Afrika
  • Gwamnatin Tinubu Ta Ƙaddamar Da Tsarin Bada Kudi Na SPARK Afrika
  • Jam’iyyar PDP Ta Sallami Manyan ’Ya’yanta Biyu A Gombe Labarai
  • NUJ Ta Yi Gargadi Kan Barazana Ga ‘Yancin Aikin Jarida A Najeriya Afrika
  • ’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Satar Wayoyin Wutar Lantarki Afrika

NFWP-SU Sun Gargadi Mata Kan ’Yan Damfara
Published: November 5, 2026 at 9:30 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shirin tallafawa mata na Najeriya mai suna Nigeria for Women Project Scale-Up (NFWP-SU) a jihar Gombe, ya yi gargaɗi ga al’umma kan wani ƙirƙirarren link da ke yawo a kafafen sada zumunta da sauran hanyoyin sadarwa, wanda ake iƙirarin cewa yana bayar da tallafin kuɗi ga mutane ƙarƙashin shirin.

Jami’ar kula da shirin a jihar Gombe, Hajiya Hauwa Ibrahim Hassan, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ta ce shirin bai da wata alaƙa da link ɗin da ake yaɗawa, tana mai bayyana shi a matsayin hanyar yaudarar jama’a.

Ta buƙaci al’umma da su yi taka-tsantsan, tare da guje wa danna link ɗin, cike bayanan sirri, bayar da bayanan asusun banki, lambobin tabbatar da sahihancin asusu ko biyan kuɗi ga duk wanda ya nemi hakan bisa sunan shirin.

Hajiya Hauwa ta bayyana cewa duk wani sahihin bayani da ya shafi tallafin kuɗi, taimakon walwala, shirye-shiryen ƙarfafa mata da sauran ayyukan shirin, za a sanar da jama’a ne ta hanyoyin sadarwa da hukumomin shirin suka amince da su.

Ta kuma buƙaci sassan aiwatar da shirin a ƙananan hukumomi (LPIUs), masu taimakawa shirin a matakin gundumomi, mambobin ƙungiyoyin mata na Women Affinity Groups (WAGs) da sauran masu ruwa da tsaki a cikin al’umma da su yi watsi da saƙon na bogi, tare da taimakawa wajen hana yaɗuwarsa.

Jami’ar ta sake jaddada aniyar shirin na kare martabarsa, tsaron waɗanda ke cin gajiyarsa da kuma tabbatar da cewa ‘yan damfara ba su yi amfani da sunan shirin wajen cutar da jama’a ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa, domin samun sahihan bayanai ko ƙarin haske kan ayyukan shirin, jama’a za su iya tuntuɓar ofishin kula da shirin na Jihar Gombe ta layin waya kyauta mai lamba 08000070777.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Tinubu Zai Ciwo Bashin Dala Biliyan 7.7

Karin Labarai Masu Alaka

Za’a Ninka Shekarun Zama A Gidan Kurkuku Ga Masu Auren Jinsi A Senegal Afrika
An Gudanar Da Jana’izar ’Yan Jaridan Da Suka Rasu A Jihar Gombe Labarai
Shugaba Trump Yace Amurka Takai Hari Kharg Tsibiri a Kasar Iran Afrika
Ferfesa Pantami Yasamu Tikitin Takarar Gwamnan Gombe A Jami’yar PDP Afrika
Kimanin Mutane 200 Ne Suka A Mutu A Wani Harin Jirgin Yakin Sojin Najeriya Afrika
Kwamitin Ardo Chindo Ya Buƙaci A Hana Mamaye Filayen Kiwo da Gandun Daji Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • NFWP-SU Sun Gargadi Mata Kan ’Yan Damfara
  • Tinubu Zai Ciwo Bashin Dala Biliyan 7.7
  • Gwamnatin Tinubu Ta Ƙaddamar Da Tsarin Bada Kudi Na SPARK
  • KADCCAM Ta Yi Gargadi Kan Illolin Kona Daji Da Gurɓata Muhalli
  • Jam’iyyar PDP Ta Sallami Manyan ’Ya’yanta Biyu A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gidauniyar Misilli Ta Tallafa Wa Yara Da Dattawa A Gombe Afrika
  • Gwamnan Jihar Kebbi Ya Amince Da Kasafin Kudi Mai Sauya Fasali Da Karfafa Rayuwar Al’umma Labarai
  • Kasashen Faransa Da Italiya Sun Nuna Rashin Amincewa Da Matakan Sojoji Amurka
  • Najeriya Ta Kai Wasan Kusa Da Na Karshe A Wasan Dambe Na Matasan Afirka Wasanni
  • Sojojin Amurka Sunfara Isowa Gabas Ta Tsakiya Amurka
  • Hukumar Zabe A Kasar Honduras Ta Sanar Da Nasry Asfura A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Shugaban Ƙasa Afrika
  • Dan Wasan Baya Na Chelsea, Disasi, Zai Yi Gwajin Lafiyarsa A Crystal Palace Wasanni
  • Athletic Club Ta Doke Atlético Madrid 3-0, Julian Alvarez Ya Koma Wasa Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.