Shugaban Ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya miƙa buƙatar neman amincewar Majalisar Dokokin Tarayya domin karɓar sabon bashin ƙasashen waje na Dala biliyan 7.7, kwatankwacin Naira tiriliyan 10.79, domin taimakawa wajen cike gibin kasafin kuɗin gwamnatin tarayya na shekarar 2026, wanda ya kai Naira tiriliyan 31.4.
Buƙatar, wadda ke ƙunshe cikin wasiƙar da shugaban ƙasar ya sanya wa hannu a ranar 26 ga Oktoba, 2026, kuma ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, an karanta ta ne a zauren Majalisar a yayin zaman ta na ranar Laraba.
Bayan karanta wasiƙar, Majalisar Dattawa ta miƙa buƙatar ga Kwamitinta mai kula da basussukan cikin gida da na ƙasashen waje domin nazari da kuma gabatar da rahoto ga Majalisar.
A cikin wasiƙar, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa an ƙididdige adadin bashin ne bisa la’akari da farashin musayar kuɗi na Naira 1,400 kan kowace Dala ɗaya.
A ƙarƙashin dokar kasafin kuɗin shekarar 2026, gwamnatin tarayya ta amince da sabon bashin Naira tiriliyan 29.2 domin cike gibin kasafin kuɗin da ake hasashen zai kai Naira tiriliyan 31.4.
Adadin ya ƙunshi bashin cikin gida na Naira tiriliyan 18.4 da kuma bashin ƙasashen waje na Naira tiriliyan 10.79, wanda ya yi daidai da Dala biliyan 7.7.
Shugaba Tinubu ya bayyana a cikin wasiƙar cewa, “Dokar kasafin kuɗin shekarar 2026 ta amince da karɓar sabon bashin Naira tiriliyan 29.2 domin taimakawa wajen cike gibin kasafin kuɗin shekarar, wanda ya kai kusan Naira tiriliyan 31.4.”
Ya ƙara da cewa buƙatar karɓar Dala biliyan 7.7 ita ce cikakkiyar ɓangaren bashin ƙasashen waje da aka tanada a cikin kasafin kuɗin.
Dangane da hanyar karɓar bashin, shugaban ƙasar ya bayyana cewa gwamnati za ta yi amfani da hanyoyin samun lamuni daban-daban a kasuwannin kuɗi na duniya, amma za a fi mayar da hankali kan sayar da takardun bashin Eurobond saboda saurin kammala cinikin da kuma damar samun makudan kuɗaɗe.
A cewarsa, sayar da Eurobond na iya taimaka wa gwamnati wajen tara kuɗaɗen da ake buƙata cikin sauri, tare da samun rangwamen kuɗin ruwa bisa sharuɗɗan da suka dace.
Shugaban ƙasar ya kuma tabbatar wa ’yan majalisar cewa Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya da Ofishin Kula da Basussukan Ƙasa (DMO) za su yi shawarwari domin tabbatar da samun mafi ƙarancin kuɗin ruwa da kuma tsawon lokacin biyan bashin bisa yanayin kasuwannin kuɗi a lokacin da za a kulla yarjejeniyar.
Dangane da yadda za a yi amfani da kuɗaɗen, Tinubu ya bayyana cewa za a karkatar da su wajen tallafa wa muhimman ayyukan more rayuwa da shirye-shiryen ci gaban tattalin arzikin ƙasa.
Fannonin da za su fi samun kulawa sun haɗa da tsaro da harkokin soja, sufuri, noma, wutar lantarki, ilimi da kuma kiwon lafiya.
Haka kuma, shugaban ƙasar ya bayyana cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) ne zai karɓi kuɗaɗen ƙasashen waje a madadin gwamnatin tarayya, lamarin da yake sa ran zai taimaka wajen ƙara yawan ajiyar kuɗaɗen waje na ƙasar, da daidaita darajar Naira, tare da ƙarfafa sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnati ke aiwatarwa.
Da yake mayar da martani kan wasiƙar, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce sabon bayanin ya maye gurbin wata buƙatar da aka gabatar a baya ta neman bashin kusan Dala biliyan 20, inda ya bayyana cewa sabuwar buƙatar ta fayyace yadda za a karɓi bashin, ba lallai sai an karɓe shi gaba ɗaya lokaci guda ba.
Akpabio ya ce ya kamata gwamnati ta nemi mafi kyawun sharuɗɗa a kasuwannin ƙasashen waje domin tabbatar da yarjejeniyar da za ta amfani ɓangarorin biyu.
Bayan amincewar Majalisar Dokokin Tarayya, ana sa ran Ministan Kuɗi kuma mai kula da tattalin arzikin ƙasa, tare da Ofishin Kula da Basussukan Ƙasa, za su jagoranci aiwatar da shirin karɓar bashin.
Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da basussukan cikin gida da na ƙasashen waje ne zai gabatar da rahotonsa ga Majalisar domin ci gaba da duba buƙatar, yayin da ake ci gaba da muhawara a ƙasar kan yawan basussukan Najeriya da yadda gwamnati ke tafiyar da kuɗaɗen ƙasa.


