Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Satar Wayoyin Wutar Lantarki Afrika
  • Tinubu Ya Shiga Cikin Ka’aba Ya Yi Addu’a Afrika
  • Gwamnatin Tarayya Ta Fara Bada Tallafin Naira Dubu Hamsin Afrika
  • Shari’ar Sirika: Odofin Ya Sha Tambayar Kwakwa Afrika
  • Ana Tsanmmanin Tinubu Ya Shiga Ka’aba Don Ganawa Da Allah Afrika

NUJ Ta Yi Gargadi Kan Barazana Ga ‘Yancin Aikin Jarida A Najeriya
Published: November 2, 2026 at 2:05 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya, hukumomin tsaro da sauran hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da gudanar da bincike tare da hukunta duk wadanda aka samu da hannu wajen cin zarafin ‘yan jarida a kasar.

Kungiyar ta yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da Shugabanta na Kasar, Alhassan Yahya, ya fitar domin tunawa da Ranar Yaki da Rashin Hukunta Masu Laifukan da ke Kai Hare-Hare kan ‘Yan Jarida ta Duniya, wadda ake gudanarwa a ranar 2 ga watan Nuwamba na kowace shekara.

NUJ ta sake jaddada kudirinta na kare ‘yancin aikin jarida, kare rayuka da mutuncin ma’aikatan kafafen yada labarai, tare da tabbatar da an yi adalci ga dukkan ‘yan jaridun da ake tsoratarwa, muzgunawa, tsarewa ba bisa ka’ida ba ko kuma kai wa hari yayin gudanar da ayyukansu.

Sanarwar ta bayyana cewa aikin jarida shi ne ginshikin dimokuradiyya mai inganci, saboda yana taimakawa wajen sanya masu rike da madafun iko a bisa ka’ida, ba wa al’ummomin da ba su da karfi damar bayyana matsalolinsu, da kuma tabbatar da hakkin jama’a na samun sahihan bayanai.

Kungiyar ta kuma bukaci jami’an tsaro da hukumomin gwamnati su rika kallon ‘yan jarida a matsayin muhimman abokan tafiyar da dimokuradiyya, maimakon daukarsu a matsayin abokan gaba.

Bugu da kari, NUJ ta bukaci hadin gwiwa tsakanin kungiyoyin kafafen yada labarai, kungiyoyin fararen hula da abokan huldar kasa da kasa domin samar da ingantattun matakan tsaro da hanyoyin agajin gaggawa ga ‘yan jaridun da ke aiki a wuraren da ke da hadari.

Kungiyar ta jaddada cewa barazana ga wani dan jarida a ko’ina, barazana ce ga dimokuradiyya a duk duniya, don haka ta yi kira ga kungiyoyin kare hakkin bil’adama da sauran al’umma da su hada kai wajen neman samar da yanayin da ‘yan jarida za su gudanar da ayyukansu cikin ‘yanci ba tare da tsoro ko nuna son kai ba.

A karshe, NUJ ta bayyana cewa babu wani dan jarida da ya kamata ya rasa tsaro, ‘yanci ko rayuwarsa saboda gudanar da aikin bayar da rahoton gaskiya.

Sanarwar mai dauke da sa hannun Shugaban NUJ na Kasa, Alhassan Yahya, ta fito ne daga Sakatariyar Kungiyar ta Kasa da ke Abuja.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya

Post navigation

Previous Post: ’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Satar Wayoyin Wutar Lantarki

Karin Labarai Masu Alaka

Rundunar ‘Yan Sanda Sun Ceto Wani Daga Hannun Masu Garkuwa Najeriya
Harin Isra’ila A Gaza Da Jirgi Maras Matuki Ya Kashe Mutane Afrika
An Kara Wa’adin Zaman Kurkuku A Senegal Ga Masu Auren Jinsi Afrika
Fitaccen Dan Jarida a Sokoto Surajo Dalhatu Sifawa Ya Rasu Najeriya
Jami’an ’Yan Sanda Daga Kamaru Da Kongo Sun Karɓi Takardun Shaida Bayan Kammala Horo Afrika
Amurka Zatayi Amfani Da Sansanonin Birtaniya Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • NUJ Ta Yi Gargadi Kan Barazana Ga ‘Yancin Aikin Jarida A Najeriya
  • ’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Satar Wayoyin Wutar Lantarki
  • Nijar Da Gabashin Libya Sun Kulla Yarjejeniya
  • Tinubu Ya Shiga Cikin Ka’aba Ya Yi Addu’a
  • Kishin Al’ada: Ministan Kamaru Mohamadou Moustafa Da Gudunmawarsa Ga Hausawa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Maryam Dan’azumi Ta Zama Abin Alfahari Ga Najeriya Bayan Lashe Gasar Alƙur’ani Ta Duniya Afrika
  • Kabiru Vice: Najeriya Zata Iya Nasara A Kan Moroko AFCON 2025. Wasanni
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane A Katsina Afrika
  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini Afrika
  • Ana Cigaba Da Ceto Masunta Daga Ruwa A Ghana Labarai
  • Shin Ko Ganawar Zelensky Da Macron Zata Haifar Da ‘Da Mai Ido? Labarai
  • Wasan Hamayya (Istanbul Derby) Fenerbahçe Da Galatasaray 1-1 Labarai
  • Gwamnatin Jamhuriyar Nijar Na Kokarin Inganta Harkokin Noman Kasar Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.