Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • NUJ Ta Yi Gargadi Kan Barazana Ga ‘Yancin Aikin Jarida A Najeriya Afrika
  • ’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Satar Wayoyin Wutar Lantarki Afrika
  • Tinubu Ya Shiga Cikin Ka’aba Ya Yi Addu’a Afrika
  • Gwamnatin Tarayya Ta Fara Bada Tallafin Naira Dubu Hamsin Afrika
  • Shari’ar Sirika: Odofin Ya Sha Tambayar Kwakwa Afrika

Jam’iyyar PDP Ta Sallami Manyan ’Ya’yanta Biyu A Gombe
Published: November 2, 2026 at 7:18 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta sanar da korar Honorobul Khamisu Ahmed Mailantarki da Honorobul Usman Aliyu Garry, dukansu daga jihar Gombe, bisa zargin aikata ayyukan cin amanar jam’iyya da karya dokokin kundin tsarin mulkinta.

A cikin wata sanarwar manema labarai da Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na PDP, Honorobul Jungudo Haruna Mohammed, ya sanya wa hannu, jam’iyyar ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne bayan kwamitin ladabtarwa ya gudanar da bincike tare da gabatar da sakamakonsa ga hukumomin jam’iyyar da abin ya shafa.

Sanarwar ta ce an same su da laifukan da suka haɗa da yi wa jam’iyya zagon ƙasa, rashin ɗa’a mai tsanani da kuma aikata abubuwan da za su iya ɓata mata suna, wanda ya saɓa wa sashe na 58(1)(a), (b), (h) da (j) na kundin tsarin mulkin PDP na shekarar 2017.

Jam’iyyar ta ƙara da cewa an bi ƙa’idojin adalci da ba wa waɗanda ake zargi damar kare kansu, kamar yadda sashe na 57(6) na kundin PDP da sashe na 36 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 suka tanada.

A cewar sanarwar, daga yanzu Khamisu Mailantarki da Usman Aliyu Garry sun daina kasancewa mambobin PDP, kuma ba su da wani haƙƙi ko gata a ƙarƙashin jam’iyyar.

A ƙarshe, PDP ta jaddada cewa babu wani mamba da ya fi ƙarfin dokokinta, tare da kira ga sauran mambobi da su kasance masu biyayya, ladabi da haɗin kai domin ƙarfafa jam’iyyar a dukkan matakai.

Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: NUJ Ta Yi Gargadi Kan Barazana Ga ‘Yancin Aikin Jarida A Najeriya

Karin Labarai Masu Alaka

Dakarun Operation Fansan Yamma Sun Ceto Mutane 48 Da Aka Yi Garkuwa Da Su Afrika
An Kaddamar Da Rigakafin Cutar HIV AIDS A Kasar Zimbabwe Kimiya
Gabanin Zaɓe: Jam’iyyun Siyasa Sun Ƙuduri Aniyar Kare Zaman Lafiyar Jihar Gombe Labarai
Mun Kwato Kimanin Naira Biliyan 40 Na Badakala A Tsawon Shekara Daya Labarai
Shugaba Tinubu Ya Taya Musulmai Murnar Sallah, Tare Da Kira Zuwa Ga Kishin Kasa Afrika
Bola Ahmed Tinubu Ya Lashe Zaben Fidda Gwani Na Shugaban Kasa A Gombe Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Jam’iyyar PDP Ta Sallami Manyan ’Ya’yanta Biyu A Gombe
  • NUJ Ta Yi Gargadi Kan Barazana Ga ‘Yancin Aikin Jarida A Najeriya
  • ’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Satar Wayoyin Wutar Lantarki
  • Nijar Da Gabashin Libya Sun Kulla Yarjejeniya
  • Tinubu Ya Shiga Cikin Ka’aba Ya Yi Addu’a

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Iran Ta Bukaci Duniya Ta Shirya Domin Fuskantar Tsadan Mai Amurka
  • An Damke Matasa Masu Gurza Kudaden Ketare Na Jabu Afrika
  • UPF Ta Bukaci Haɗin Gwiwa Da NERDC Domin Gina Al’umma Mai Zaman Lafiya Afrika
  • Salmanu: Ci Gaban Wikki Tourist FC Shine A Gaba Na Wasanni
  • Shugaban Amurka Ya Ya Bukaci Iran Ta Mika Wuya Afrika
  • Gwamnatin Jihar Neja Ta Soke Lasisin Mallakar Wasu Manyan Filaye A Jihar Labarai
  • Sama Da Zawiyya 100 Ne Suka Samu Tallafin Kayan Abinci Daga Al’mustapha Haji Sufi Labarai
  • Hukumar DSS Ta Sake Kama Abubakar Malami Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.