Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Kotu Ta Kori Shugabancin ADC Na Sanata David Mark, Ta Soke Takarar Atiku Abubakar. Afrika
  • Tinubu Zai Ciwo Bashin Dala Biliyan 7.7 Afrika
  • Gwamnatin Tinubu Ta Ƙaddamar Da Tsarin Bada Kudi Na SPARK Afrika
  • Jam’iyyar PDP Ta Sallami Manyan ’Ya’yanta Biyu A Gombe Labarai
  • NUJ Ta Yi Gargadi Kan Barazana Ga ‘Yancin Aikin Jarida A Najeriya Afrika

Gidauniyar Misilli Ta Tallafa Wa Yara Da Dattawa A Gombe
Published: September 21, 2026 at 8:35 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gidauniyar Ci gaban Al’umma ta Misilli ta shigar da ƙarin yara 60 cikin makarantun firamare a Jihar Gombe, lamarin da ya sa adadin yaran da suka amfana da tallafin ilimi na gidauniyar tun bayan kafuwarta ya kai 210.

Mai kula da ayyukan gidauniyar, Yusuf Hamza, ne ya bayyana hakan a yayin bikin karɓar rukunin yara na huɗu da gidauniyar ta ɗauka, wanda aka gudanar a gidan wanda ya kafa gidauniyar, Alhaji Isma’il Uba Misilli, da ke unguwar Dawaki a Gombe.

Yusuf Hamza ya ce an kafa gidauniyar ne a shekarar 2018, domin mayar da hankali kan ilimi, kiwon lafiya da kuma ci gaban al’umma, inda ya bayyana ilimi a matsayin babban ɓangaren ayyukan gidauniyar.

Ya ce gidauniyar ta tallafa wa yara daga iyalai masu ƙaramin ƙarfi ta hanyar shigar da su makarantu, ba su tallafin karatu da kuma fom ɗin JAMB, tare da haɗin gwiwa da shirin AGILE wajen samar da kayan karatu.

Wakilin Kwamishinan Ilimi na jihar Gombe, Alhaji Abdullahi Abubakar, tare da wasu jami’an gwamnati, sun yaba wa gidauniyar bisa yadda take taimaka wa gwamnati wajen bunƙasa fannin ilimi.

Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, Barrister Sani A. A. Haruna; Kwamishinan Kuɗi, Alhaji Muhammad Gambo Magaji; Shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe, Farfesa Abubakar Bappah Garkuwa; da ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Gombe North, Ali Baba Manu, sun yi kira ga daidaikun mutane da ƙungiyoyi da su tallafa wa gidauniyar domin ta faɗaɗa ayyukanta.

A nasa ɓangaren, wakilin shirin AGILE na Jihar Gombe, Alhaji Jabiru Kilawa, ya yaba da haɗin gwiwar da ake samu, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen inganta damar samun ingantaccen ilimi, musamman ga ’yan mata.

Sakataren Ilimi na Ƙaramar Hukumar Gombe, Hamza Baba, ya ce samun ilimi haƙƙi ne na kowane yaro, yana mai bayyana cewa gwamnatin jihar, ta hannun Hukumar SUBEB, ta shigar da dubban yaran da ba sa zuwa makaranta cikin tsarin karatu.

Shi ma mai ba Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, shawara kan harkokin Almajirai kuma dattijo mai kishin al’umma, Alhaji Yaya Hammari, ya yaba wa gidauniyar bisa ci gaba da tallafa wa marasa ƙarfi da sauran masu buƙatar taimako a cikin al’umma.

Da yake jawabi, wanda ya kafa gidauniyar, Alhaji Isma’il Uba Misilli, ya ce an kafa shirin ne domin tallafa wa ƙoƙarin gwamnati wajen samar da dama ga yara marasa galihu, marayu da sauran masu rauni a cikin al’umma.

A yayin bikin, an bai wa wasu daga cikin ɗaliban da suka nuna ƙwazo kekuna, jakunkunan makaranta da littattafan karatu.

Haka kuma, gidauniyar ta bai wa mata da tsofaffi 200 tallafin ƙarfafa tattalin arziƙi, inda kowannensu ya samu naira dubu goma.

Gidauniyar ta ce za ta ci gaba da ayyukan tallafa wa ilimi da sauran shirye-shiryen ci gaban al’umma domin taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi a Jihar Gombe.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Laccar Bagauda Kaltho Ta Jaddada Muhimmancin Yaƙi Da Yaɗa Labaran Karya
Next Post: NIHSA Ta Yi Gargadin Ambaliyar Ruwa A Jihohi 15

Karin Labarai Masu Alaka

Mataimakin Shugaban Kasar Amurka Ya Gana Da Wasu Wakilai Amurka
Nan Gaba Kadan Kwallon Badminton Zata Samu Karbuwa Kamar Kwallon Kafa A Duniya Labarai
Shugabannin Kasashen Afirka Ta Tsakiya Sun Kamallah Taron Koli Afrika
Dakaru Sun Hallaka ’Yan Ta’adda Masu Yawa – DHQ Afrika
Sabuwar Shekarar Musulunci: Shugaban Gwamnonin Arewa Ya Yi Kira Da A Yawaita Addu’o’i Da Haɗin Kai Afrika
Masu Luwadi Na Fuskantar Tara Da Daurin Shekaru 20 A Nijar Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Kotu Ta Kori Shugabancin ADC Na Sanata David Mark, Ta Soke Takarar Atiku Abubakar.
  • NFWP-SU Sun Gargadi Mata Kan ’Yan Damfara
  • Tinubu Zai Ciwo Bashin Dala Biliyan 7.7
  • Gwamnatin Tinubu Ta Ƙaddamar Da Tsarin Bada Kudi Na SPARK
  • KADCCAM Ta Yi Gargadi Kan Illolin Kona Daji Da Gurɓata Muhalli

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamna Abba Kabir Ya Zabi Garo A Matsayin Mataimaki Afrika
  • An Murkushe Wani Yunkurin Juyin Mulki A Jamhuriyar Benin Afrika
  • Dakarun Gwamnatin Kasar Sham Tayi Mamaya Zuwa Gabashin Kasar Labarai
  • Gwamnan Jihar Kebbi Ya Amince Da Biyan Hakkokin Tsofin Ma’aikata 800 Labarai
  • Tinubu Na Kokarin Rage Tsadar Sufuri Ta Hanyar Shirin CNG Afrika
  • NUJ: Akwai Bukatar Samar Da Inshorar Lafiya Ga ‘Yan Jarida A Najeriya Rediyo
  • TIC Dutse Ta Nemi Ƙarin Tallafin Gwamnatin Jigawa Don Faɗaɗa Ayyukanta Afrika
  • Gwamnatin Gombe Zata Inganta Samar Da Wuta Wajen Amfani Da Hasken Rana Kimiya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.