Gidauniyar Africa Media Development Foundation (AMDF) ta yi kira ga ’yan jarida da kafafen yaɗa labarai da su ƙara ƙaimi wajen tabbatar da sahihancin bayanai, musamman yayin da Najeriya ke tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
Gidauniyar ta bayyana hakan ne a yayin bikin Lacca ta 8 ta Bagauda Kaltho Media Lecture, wadda aka gudanar ranar 19 ga Satumba, 2026, domin tunawa da marigayi ɗan jaridar bincike, Bagauda Kaltho.
Taken laccar shi ne “Courageous Journalism, Press Freedom and the Challenge of Election Misinformation Ahead of Nigeria’s 2027 General Elections”, wato aikin jarida mai ƙarfin hali, ’yancin manema labarai da ƙalubalen yaɗuwar bayanan ƙarya gabanin babban zaɓen Najeriya na 2027.
Babban jawabin taron ya fito ne daga Mista Dapo Olorunyomi, Mawallafi kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Premium Times, wanda ya yi nazari kan gudunmawar da aikin jarida ya bayar wajen samun ’yancin kai, bunƙasa dimokuraɗiyya da kuma adawa da mulkin soja a Najeriya.
Olorunyomi ya kuma yi tsokaci kan sauye-sauyen da fasahar zamani ta kawo wa harkar yaɗa labarai, da kuma matsalolin tattalin arziki da ke fuskantar kafafen yaɗa labarai da ’yan jarida.
A cikin sanarwar da aka fitar bayan taron, mahalarta sun bayyana damuwa kan yadda amfani da fasahar Artificial Intelligence (AI) ke ƙara sauƙaƙa ƙirƙirar hotuna, bidiyoyi da sautukan bogi, ciki har da sakamakon zaɓe na ƙarya da ake iya yaɗawa a kafafen sada zumunta.
Sun ce saurin yaɗuwar bayanai a kafafen sada zumunta na iya sa labaran ƙarya da yaɗa bayanan da aka ƙirƙira su bazu cikin sauri fiye da yadda ’yan jarida da masu tantance sahihancin bayanai za su iya mayar da martani.
Taron ya kuma yi nuni da cewa ’yan jarida na ci gaba da fuskantar ƙalubalen doka da na hukumomi, ciki har da damuwar da ake da ita kan yadda ake amfani da wasu tanade-tanaden dokar Cybercrimes Act da sauran tsofaffin dokokin da ka iya takaita ’yancin aikin jarida.
AMDF ta jaddada muhimmancin horar da ’yan jarida akai-akai kan tantance sahihancin bayanai, amfani da fasahar zamani, Artificial Intelligence da aikin jarida na bincike.
Ta kuma yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su samar da ingantattun hanyoyin tantance bayanai kafin su wallafa su, maimakon dogaro kawai da bayanan da ke yawo a kafafen sada zumunta.
Haka kuma, taron ya bukaci gwamnati da hukumomin gwamnati su tallafa wajen samar da ingantattun hanyoyin tantance bayanai tare da ƙarfafa kyakkyawar alaƙa tsakanin jami’an tsaro da kafafen yaɗa labarai.
An kuma yi kira ga hukumomin da suka dace da su sake duba tsofaffin dokokin da ke kawo cikas ga ’yancin aikin jarida, tare da yin gyare-gyaren da suka dace domin tabbatar da yanayin da aikin jarida mai inganci zai iya gudana.
A bangaren kamfanonin fasaha da kafafen sada zumunta, taron ya bukaci su haɗa kai da ’yan jarida, ƙungiyoyin farar hula da hukumomin gwamnati wajen dakile yaɗuwar bayanan ƙarya da kuma samar da hanyoyin gano bayanan da aka ƙirƙira ta amfani da AI.
Taron ya kuma jaddada muhimmancin ilimin kafofin yaɗa labarai da tunani mai zurfi, inda aka buƙaci jama’a su koyi dakatawa, tantancewa da kuma tambayar sahihancin bayanan da suke karɓa kafin su sake yaɗa su, musamman a lokacin zaɓe.
Laccar ta kuma yaba da shirye-shiryen da ke bai wa matasa ’yan jarida horo domin su dace da sauye-sauyen da ke faruwa a harkar yaɗa labarai, tare da jaddada muhimmancin ilimin aikin jarida, ɗabi’un sana’a da ƙwarewar fasahar zamani.
Taron ya buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki, da suka haɗa da ’yan jarida, kafafen yaɗa labarai, gwamnati, kamfanonin fasaha, ƙungiyoyin farar hula, malamai da jama’a, su haɗa kai wajen inganta yanayin yaɗa bayanai gabanin zaɓen 2027.
Sanarwar ta ce kare sahihancin aikin jarida ba nauyin ’yan jarida kaɗai ba ne, domin jama’a ma suna da rawar takawa wajen bambance ingantattun bayanai da waɗanda aka ƙirƙira.
An kuma jaddada cewa tarihin marigayi Bagauda Kaltho na ci gaba da zama abin tunatarwa kan haɗarin da ’yan jarida suka sha fuskanta wajen neman gaskiya da tabbatar da riƙon shugabanni da hukumomi da alhaki.
An fitar da sanarwar ne a ƙarshen Laccar Bagauda Kaltho ta 8 da aka gudanar ranar 19 ga Satumba, 2026, kuma Titus Usman, Mawallafin Jewel Treasure Newspaper, da Sekyen Dadik, Babban Daraktan AMDF, ne suka sanya hannu a kanta.


