Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta kori shugabannin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) karkashin jagorancin Sanata David Mark, tare da soke dukkan matakan da suka dauka a madadin jam’iyyar.
Matakan da kotun ta soke sun hada da tsayar da tsohon mataimakin shugaban ƙasar nan, Alhaji Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027.
Tun da farko, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta wallafa sunan Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, wanda shi kuma ya zaɓi tsohon gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, a matsayin abokin takararsa.
Sai dai a hukuncin da mai shari’a Peter Lifu ya yanke ranar Alhamis, kotun ta bayyana cewa kwamitin riƙon ƙwarya na ADC ƙarƙashin Sanata David Mark ya kasance ba bisa ƙa’ida ba, inda ta ce kwamitin ne ya shirya zaɓen fitar da gwani da ya samar da Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar.
Kotun ta yanke hukuncin ne bayan ta amince da ƙarar da tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa mai kula da shiyyar Arewa maso Gabas, Nafiu Bala Gombe, ya shigar.
Nafiu Bala Gombe ya garzaya kotu ne domin ƙalubalantar tsarin da kwamitin Sanata David Mark ya bi wajen karɓar shugabancin jam’iyyar.
Ya bayyana cewa bayan murabus ɗin tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Cif Ralph Nwosu, shi ne ya cancanci karɓar ragamar shugabancin ADC.
Saboda haka, ya roƙi kotun da ta soke dukkan matakan da shugabancin Sanata David Mark ya ɗauka a madadin jam’iyyar.
Waɗanda aka ambata a matsayin waɗanda ake ƙara a shari’ar mai lamba FHC/ABJ/CS/1819/2025 sun haɗa da jam’iyyar ADC, INEC, Sanata David Mark, Ogbeni Rauf Aregbesola da Cif Ralph Nwosu.
Mai ƙarar ya kuma buƙaci kotun da ta hana Sanata David Mark da Rauf Aregbesola ci gaba da bayyana kansu a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa da sakatarenta, bisa hujjar cewa zaɓen da ya kai su muƙaman ya saɓa wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar da tanade-tanaden dokar zaɓe.
Kotun ta amince da buƙatun mai ƙarar, tare da bayar da umarnin da ya dace da su.
Wannan hukunci na iya haifar da sauye-sauye a siyasar ƙasar nan, musamman ganin cewa an tsara gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a ranar 16 ga watan Janairun 2027.
Sai dai tuni jam’iyyar ADC ta bayyana aniyarta ta ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin a kotun ɗaukaka ƙara.
Da yake mayar da martani kan hukuncin, Sakataren Jinƙai na Ƙasa na ADC, Mista Nkemakolam Ukandu, wanda daga baya aka shigar da shi cikin shari’ar a matsayin mai ruwa da tsaki, ya ce jam’iyyar za ta ƙalubalanci hukuncin a kotun ɗaukaka ƙara.
Wannan ci gaban na zuwa ne ƙasa da sa’o’i 24 bayan ɗan takarar jam’iyyar, Atiku Abubakar, ya gudanar da gagarumin gangamin yaƙin neman zaɓe a Jihar Sokoto, a wani ɓangare na shirye-shiryensa na neman shugabancin ƙasar a zaɓen 2027.


