Al’umma a Kano dake arewacin Najeriya na ci gaba da jimamin rasuwar fitaccen mai sharhi kan harkokin jama’a, ɗan jarida kuma marubuci, Bello Muhammad Sharada, wanda ya rasu yana da shekaru 56.
Marigayin ya rasu ne a ranar Asabar a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.
Bello Sharada ya shahara wajen yin sharhi da nazari kan al’amuran siyasa da sauran batutuwan da suka shafi Najeriya, musamman ta kafafen sada zumunta, ciki har da Facebook.
Ya kasance mai goyon bayan siyasar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, kuma ya shafe shekaru yana bayar da gudunmawa wajen bunkasa muhawarar jama’a ta hanyar rubuce-rubuce da sharhinsa kan siyasa da sauran al’amuran ƙasa.
Bayan rasuwarsa, abokai, abokan aiki da sauran al’umma sun bayyana alhininsu, inda suka bayyana marigayin a matsayin mutum mai kishin rubutu da bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen wayar da kan jama’a.
An gudanar da jana’izarsa da misalin ƙarfe 8:00 na safe ranar Lahadi a Sharada Fegi, cikin ƙaramar hukumar Kano Municipal, bisa tsarin addinin Musulunci.
Marigayin ya rasu ya bar iyalansa da ’yan uwa da abokan arziki.


