Kasar China ta ce tana adawa da matakin nuna fin karfi, bayan Amurka ta bada umurnin tare dukkan jiragen ruwan jigilar mai da aka kafa ma takunkumi wadanda ke kokarin zuwa ko fitowa daga kasar venezuela mai arzikin man fetur.
China ita ce ta fi kowace kasa sayen danyen man kasar Venezuela, inda a wannan watan ake sa ran cewa a kowace rana zata na saye ganga dubu 600 na man Venezuela.
Ministan harkokin wajen China, Wang Yi, ya fadawa takwaransa na Venezuela a tattaunawar da suka yi ta wayar tarho cewa China tana yin adawa da duk wani matakin nuna fin karfi da wata kasa zata so nunawa, sannan tana goyon bayan kasashe wajen kare mutuncin kasarsu.
Wang bai ambaci sunan Amurka ko shugaba Trump a bayanin da aka bayar na tattaunawar ba, haka kuma bai fadi irin tallafin da China zata iya ba Venezuela ba.
Shugaba Nicolas Maduro yace Amurka tana neman mallakar danyen man fetur na Venezuela ne, kuma girke sojojin da take yi a yankin na neman hambarar da shi daga kan mulki ne.
Amurka dai ta ce tana yakar safarar muggan kwayoyi ne zuwa cikin kasarta.


