Kotu a kasar Tunisia ta aike da wani dan majalisa gidan wakafi har zuwa wata takwas saboda wallafe-wallafen da ya yi a kafofin sada zumunta na batanci ga shugaban kasar Kais Saied.
Dan majalisar mai suna Ahmad Saidani, wanda da yake goyon bayan shugaban kasar, ya sauya ra’ayin sa, inda ya zargi shugaban kasar da neman yanke shawara shi kadai a duk Wasu harkoki, kuma daga baya idan an samu matsala ya dorawa wasu lefi.
An Zabi Saidani ne a matsayin dan majalisa a karshen shekarar 2022, a wani zabe na ‘yan majalisa da aka gudanar bayan da shugaba Kais Saied ya soke majalisar a shekarar 2021.


