A Kasar Australia, mutane da dama ne suka taru ranar Talata domin nuna alhinin su a harin da wasu mutane biyu suka kai a gabar ruwan kasar, suka kashe akalla mutane 16 ranar lahadi.
Har ma aka ji jakadan Is’raila a kasar yana kira ga hukumomin kasar a Sydney su dauki matakan da suka wajaba wajen kare rayukan yahudawa a kasar.
A halinda ake ciki kuma, mutumin da ake yi wa lakabin gwarzo, saboda kwace bindiga daga hanun daya daga cikin maharran, yana ci gaba da jinya a asibiti, yayinda asusun gudumawa da aka kafa dominsa, ya sami tallafin jama’a da ya haura dala milyan daya na kudin Australia, kimanin dalar Amurka dubu dari bakwai da arba’in da hudu. 
Dan shekaru 43 da haifuwa Ahmed Ahmed ya afkawa daya daga cikin maharan, ya kwace binidgar dake hannunsa. amma daya maharin ya harbi Ahmed a hanu sau biyu sannan anyi masa tiyata, kuma yana samun sauki.
Wannan harin shine mafi muni cikin shekaru 30 a Australia.


