Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Ana Cigaba Da Bincike Game Da Mutuwar Matar Da Likita Ya Manta Almakashi A Cikinta A Kano
Published: January 14, 2026 at 8:15 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar kula da asibitocin jihar Kano ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan mutuwar wata matar aure mai suna Aishatu Umar, wadda ake zargin ta rasu sakamakon sakaci a aikin likitanci bayan an yi mata tiyata a asibitin Abubakar Imam.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’ar hulɗa da jama’a ta hukumar, Samira Suleiman, ta fitar a ranar Talata.

“Kwamitin Kula da Asibitocin jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Babban Sakatare, Dakta Mansur Mudi Nagoda, ya lura da rahoton da ya tayar da hankula game da rasuwar Aishatu Umar.

“Muna miƙa ta’aziyyarmu ga iyalanta da masoyanta. Babban Sakatare ya bayar da umarnin a gaggauta gudanar da cikakken bincike kan zargin da aka yi a asibitin Abubakar Imam domin gano gaskiya da abin da ya faru,” in ji ta.

Hukumar ta tabbatar wa jama’a cewa binciken zai kasance a bayyane, ba tare da son zuciya ba, kuma cikin ƙwarewa, tare da ƙara da cewa za a ɗauki matakan da suka dace bisa ƙa’idoji idan aka tabbatar da wani sakaci.

Idan za iya tunawa cewa an rawaito marigayiya Aishatu Umar ta rasu ne bayan abin da iyalanta suka bayyana a matsayin zargin sakaci a aikin likitanci bayan an yi mata tiyata a asibitin.

A cewar wani ɗan uwanta, Mohammed, wanda ya wallafa a shafin Facebook, marigayiya Aishatu, matar aure mai ‘ya’ya biyar, ta rasu da misalin ƙarfe 1 na dare a ranar Talata bayan ta sha fama da ciwon ciki mai tsanani tun bayan tiyatar da aka yi mata a watan Satumba na 2025.

“Ta fara korafin ciwon ciki mai tsanani wanda ya ci gaba har tsawon watanni. Ta sha wannan ciwo na tsawon watanni huɗu,” in ji Mohammed.

Ya yi zargin cewa duk da yawan komawarta asibitin, ma’aikatan lafiya suna ba ta magungunan rage zafi ne kawai su sallame ta ba tare da yin cikakken bincike ba.

Mohammed ya ƙara da cewa sai kwanaki biyu kacal kafin rasuwarta ne aka yi mata cikakkun gwaje-gwaje da hotunan bincike (scanning), waɗanda suka nuna wai an bar almakashi guda biyu a cikin jikinta tun lokacin tiyatar watan Satumba.

“An fara shirye-shiryen yin gyaran tiyata, amma lokacin nata ya ƙare,” in ji shi.

Najeriya

Post navigation

Previous Post: Wasu Lauyoyi Sunyi Murabus Yayin Gudanar Da Wata Shari’a A Kasar Amurka
Next Post: Fitaccen Dan Jarida a Sokoto Surajo Dalhatu Sifawa Ya Rasu

Karin Labarai Masu Alaka

Najeriya Da Dubai Zasu Karbi Bakoncin Taron Zuba Hannayen Jari Najeriya
Rashin Tsaro: Gwamnati Ta Bada Umarnin Daukar Ma’aikata Sama Da 94,000 Najeriya
Soyinka Ya soki Yawan Jami’an Tsaron Da Ake Bai Wa Seyi Tinubu Najeriya
Burkina Faso Ta Sako ‘Yan Najeriya 11 Najeriya
Gwamnatin Sokoto Tabada Umarnin Biyan Albashin Watan Fabrairu Labarai
Shugaban Kasar Najeriya Ya Gabatar Da Kudi Fiye Da Naira Triliyan 58 A Matsayin Kasafin 2026 Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango
  • Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi
  • Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ga Fili Ga Doki Najeriya
  • Tattalin Arzikin Kasar Congo Ya Bunkasa Labarai
  • Hukumar Kare Hakkin ‘Yan Jarida Tace Isra’ila Ce Ta Kashe ‘Yan Jarida Kashi Biyu Bisa Uku Labarai
  • Magoya Bayan Nice Sun Kai Hari Wa ‘Yan Wasansu Wasanni
  • Yeriman Ingila Ya Mayarwa Trump Martani Amurka
  • Koriya Ta Arewa Ta Gudanar Da Gwajin Makami Mai Linzami Tsaro
  • Amurka Na Gargadin Rwanda Da Ta Mutunta Alkawali Afrika
  • Kasar Ukraine Ta Yabawa Tarayyar Turai Bisa Bata Tallafi Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.