Kasar Djibouti zata gudanar da zaben shugaban kasa a yau Jumu’a, inda ake ganin shugaba mai ci a yanzu Isma’il Omer Guelleh zai lashe, ya ci gaba da mulkin da ya shafe shekaru 27 yana kai, bayan da majalisar kasar ta soke dokar data kayyade shekarun masu tsayawa takara, wadda da akwai ta zata haramta masa tsayawa.
Guelle me shekara 78 ya karbi ragamar mulkin kasar tun a shekarar 1999, bayan an zabe shi da ya maye gurbin kawun sa Hassan Gouled, wanda shine shugaban kasar na farko bayan ta samu ‘yancin kan ta a shekara 1977.
Kasar dake gabashin Afirka, nada zaman lafiya bisa ga makwabtan ta Somalia da Habasha.


