Hukumomi a jihar Rhode Island a Amurka sun sake rokon jama’a ranar talata da su taimaka musu da wajen gano dan bindigar da ake zaton shine aka gan shi a wasu hotunan bidiyo, wanda kuma ake zargin shine ya bindige ya kashe wasu dalibai biyu na Jami’ar Brown a karshen mako.

A yayin da aka shige kwanaki uku ana farautar dan bindigar, kuma jama’a suna ci gaba da zaman dar-dar, jami’ai a birnin Providence na Rhode Island sun ce har yanzu ba su gane ko wanene dan bindigar ba.
Sun nuna wasu hotunan bidiyo da suka nuna mutumin yana kai gwauro da mari a kusa da inda aka yi harbin a ranar asabar, yana sanye da kaya masu duhu, kuma ya rufe fuskarsa da kyalle.
Baturen ‘yan sanda na birnin Providence, Oscar Perez, yace masu bincike suna fatan cewa wani wanda ya san mutumin zai iya gane shi ta hanyar ganin yadda yake tafiya da motsi da jikinsa.
Yace ‘yan sanda suna da shaidar cewa an ga wannan mutumin a wurin da misalin karfe 10.30 na safiyar asabar, fiye da awa biyar ke nan kafin a yi harbin.
Jami’ai suka ce suna da kwarin guiwar cewa mutumin da aka gani a wadannan hotunan bidiyo shine dan bindigar.


