Asusun bada lamuni na duniya watau IMF a takaice yace ya cimma yarjejeniya da Masar a wasu matakai na biyar da na shida na rance, wanda zai sa asusun ya baiwa Misra dala bilyan 2.5.
Asusun yace ya hade rukuni na biyar dana shida karkshin shirin bitar rancen, saboda hakan ya baiwa hukumoin Masar damar aiwatar da sharuddan da suke kunshe cikin shiri bada lamunin, Ha kazalika asusun yace sun cimma daidaito da Masar na sakar mata kudi dala bilyan daya da milyan dari uku.
Duk da haka, sai majalisar gudanarwar asusun ta amince da wadannan matsaya da aka cimma da masar.
Hukumomin Misra sun amince da karbar bashi daga hanun IMF cikin watan Maris a bara, na kudi dalar Amurka bilyan takwas a tsawon shekaru hudu, a lokacin Masar tana fama da hauhawar farashin kayayyaki, da karancin kudaden waje, a lokacin Masar tana fuskantar hauhawar farashin kaya da ya kai maki 38 a watan satumban shekara ta 2023, amma zuwa watan satumban bana, hauhawar farashin ya ragu zuwa maki 12.
Hakanan karancin kudaden ketare da kasar ta fuskanta sun sassauto sakamakon rancen da IMF ta bata, karin samun kudaden shiga daga masu yawon bude ido, da kuma wasu yarjejeniyoyin kasuwanci data kulla da ksashen dake yankin Gulf, musamman hadaddiyar daular larabawa UAE.


