Babban hafsan hafsoshin sojan kasar Libya, Mohammed Ali Ahmed al-Haddad, ya mutu a lokacin da jirgin saman da yake ciki yayi hatsari bayan tashin sa daga Ankara, babban birnin Turkiyya ranar talata da maraice.
Fira ministan gwamnatin kasar Libya wadda kasashen duniya suka amince da ita, Abdulhamid Dbeibah, ya fada cikin wata sanarwa cewa akwai wasu jami’an gwamnatin ta Libya su hudu a cikin wannan jirgi.
Fira ministan yace wannan lamari ya faru ne a lokacin da babban hafsan tare da tawagarsa suke komawa gida a bayan ziyarar aiki a babban birnin na Turkiyya.
Yace sauran wadanda suke cikin wannan jirgi sun hada da kwamandan rundunar sojojin kasar ta Libya, da daraktan hukumar kere-keren kayan soja, da wani mai bawa babban hafsan shawara tare da wani mai daukar hoto daga ofishinsa.
Ministan harkokin cikin gidan Turkiyya, Ali Yerlikaya ya fada a shafin sada zumunci na X cewa jirgin ya tashi a kan hanyar komawa Tripoli daga filin jirgin saman Esenboga na Ankara da karfe 5 da minti 10 na yamma agogon kasar, kuma ya bace da karfe 5 da minti 52. Ya ce hukumomi sun gano inda jirgin ya fadi a gundumar Haymana ta lardin Ankara.
Yace wannan jirgi kirar Dassault Falcon-50, ya nemi a ba shi iznin saukar gaggawa a lokacin da yake wucewa ta samaniyar Haymana, amma sai aka kasa samunsa ta rediyo.
Ba a san abinda ya haddasa faduwar jirgin ba, amma Ministan shari’a na Turkiyya, Yilmaz Tunc, yace an kaddamar da bincike.
Wani karamin ministan harkokin siyasa da sadarwa a gwamnatin hadin kan kasa ta Libya, Walid Ellafi, ya fadawa kafar sadarwar Al-Ahrar ta libya cewa jirgin na haya ne daga wani kamfani a kasar Malta sannan yace jami’ai ba su da cikakken bayani a game da tarihin wannan jirgi ko wanda ya mallake shi, amma dai abu ne da zai fito a binciken da aka kaddamar.
Gwamnatin kasar wadda ita ce kadai MDD ta amince da ita a zaman hukuma a kasar libya, ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku a kasar.


