Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Bankin Duniya Zaibawa Kasar Mozambique Lamunin Dala Bilyan Shida
Published: February 24, 2026 at 11:03 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Bankin duniya yana shirin zai baiwa Mozambique rancen kudi dala bilyan shida galibi da sassaucin gaske domin ayyukanta na samar da abubuwan more rayuwa ga al’umarta cikin shekaru biyar masu zuwa, kamar yadda wani babban jami’in bankin ya fada ranar Litinin.

Baitul malin gwamnatin kasar yana fuskantar mawuyacin hali, har ma asusun bada lamuni na duniya da ake kira IMF a takaice yayi gargadi cikin makon jiya kan yadda yawan bashi yake raunata tattalin arzikin kasar.

“Bankin ya tanadi dala bilyan uku, kuma muna sa ran hada kan wasu dala bilyan uku,” inji Fily Sissoko, darektan yanki na bankin duniya mai kula da kasashen Mozambique, Madagascar, Mauritius, Sechelles, da Comoros, yayinda yake magana da manema labarai.

Bankin mai helkwata a birnin Washington DC, yana kuma fatar samar da wasu kudade dala bilyan hudu domin tallafawa ‘yan kasuwa.

Wannan kawance ko hadin kai, burinsa shine tabbatar da karfafa harkokin tattalin arziki, da zimmar ci gaba da ganin tattalin arziki yana farfadowa, kamar yadda ministan harkokin kudin kasar Carla Louveira ta fada.

Labarai, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Rundunar Sojin Amurka Sunfara Ficewa Daga Kasar Sham
Next Post: Aikin Layin Dogon Kasar Uganda Zai Hade Kasar Da Tanzania Da Kwango

Karin Labarai Masu Alaka

Indiya Da Brazil Sun Kulla Yarjejeniyar Cinikayya Afrika
Ethiopia Tana Horas Da Dakarun RSF A Wani Sansani Afrika
Asusun IMF Ya Bukaci Afirka Ta Kudu Ta Rage Bashin Da Suke Karba Afrika
Gwamnatin Bauchi: Ta Kaddamar Da Kwamitin Ma’adanai Labarai
Wasan Hamayya (Istanbul Derby) Fenerbahçe Da Galatasaray 1-1 Labarai
Rikici Ya Lafa A Kasar Iran Bayan Daukar Matakai Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango
  • Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi
  • Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • An Sako Ɗaliban Makaranta 130 Da Aka Sace A Jihar Neja  Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Hukumar Hakar Ma’adanai A Kasar Zambiya Ta Dakatar Da Ayyukanta Kimiya
  • Gwamnatin Gombe Ta Aza Tubalin Gina Sakatariyar Gundumomin Cigaba (LCDAs) Labarai
  • An Kafa Majalisar Kotun Sulhu Ta Kano Labarai
  • Shugaban Kasar Ivory Coast Yayi Sauye-Sauye A Majalisar Ministocin Kasar Siyasa
  • Akwai Shakku Akan Sanin Wacce Kungiyar Kwallon Kaface Zata Lashe Gasar Kofin Afirka Da Akeyi A Morocco Nishadi
  • Jihar Kano Tayi Rashin ‘Yan Majalisu Biyu Najeriya
  • An Gano Gawar Dan Yawon Bude Ido A Kasar Chadi Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.