Gwamnatin jihar Gombe a Najeriya ta sanar da cewa mutum 11 sun kamu da zazzabin Lassa, inda mutum ɗaya ya rasu.

Kwamishinan Ma’aikatar Lafiya a Jihar Gombe, Dokta Habu, ne ya bayyana hakan yayin wani taron saka ido da mayar da martani kan barkewar cututtuka da aka gudanar a Gombe.

Dokta Habu ya ce marigayin ya fara nuna alamun zazzabin Lassa ne yayin da yake jihar Taraba, kafin daga bisani a turo shi Asibitin Koyarwa na Tarayya (FTH), Gombe, domin jinya.
Ya kara da cewa, ta fuskar kididdigar lafiyar jama’a, lamarin ana daukarsa a matsayin na jihar Taraba.
“An kula da marasa lafiyar a Gombe, amma asalin zazzabin daga Taraba ya fito, an mayar da lambar EPID zuwa jihar Taraba,” in ji shi.
Ya bayyana cewa yawancin mutanen da aka tabbatar sun kamu da zazzabin Lassa na daga cikin mutanen da ke zuwa jihar Taraba domin aikin noma.
Kwamishinan ya jaddada cewa ko da mutum guda ne aka tabbatar ya kamu da cutar, ana daukar sa a matsayin barkewar cuta, saboda tsananin hadarinta.
Dokta Habu ya ce Gombe ta samu nasarar dakile barkewar cututtuka da dama sakamakon shiri tun kafin lokaci, tare da saurin daukar mataki da hadin gwiwa da hukumomi kamar Hukumar Kula da Cututtuka ta Kasa (NCDC), Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da UNICEF.
Ya ce an kira taron yankin ne domin karfafa tsarin sa ido da daukar mataki kan barkewar cututtuka a jihohin yankin, biyo bayan yawaitar barkewar cututtuka a jihohin Adamawa, Taraba, Bauchi da Plateau.
A karshe, kwamishinan ya bukaci a rika gano cututtuka da wuri, bayar da rahoto cikin gaggawa, da karfafa hadin kai tsakanin jihohi, domin dakile yaduwar zazzabin Lassa da sauran cututtuka masu yaduwa a cikin al’umma


