Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya daga kasar Indonesia sun rasa rayukan su a wasu hare-hare biyu a kudancin Lebanon, bayan rincabewar fada a karshen mako, inda ‘yan jarida da ma’aikatan jinya suka rasa rayukan su sakamakon harin da Isra’ila ta kai wajen.
An kashe dakarun na kiyaye zaman lafiya biyu ranar Litinin bayan da wani abu da yayi bindiga da ba’a san daga inda ya zo ba ya tarwatsa motar su kusa da Bani Hayyan a kudancin Lebanon, a cewar ofishin dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya. Sojoji biyu kuma sun samu rauni.
Kafin wannan kuma, wani sojan dan Indonesia ya rasa ran sa ranar Lahadi yayin da wani makami ya fashe kusa da inda sojojin suke a kauyen Adchit al Qusayr dake kudancin Lebanon.


