ECOWAS za ta kafa rundunar haɗin gwiwar yaƙi da ta’addanci domin fuskantar ta’addanci da matsalar rashin tsaro
Ƙungiyar habaka tattalin arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka wato (ECOWAS) ta bayyana shirin kafa rundunar tsaro ta haɗin gwiwa domin fuskantar ƙaruwar barazanar ta’addanci a yankin.
Shugaban Hukumar Shugabannin ECOWAS kuma Shugaban Ƙasar Saliyo, Julius Maada Bio, ne ya sanar da hakan a Zama na 68 na Majalisar Shugabannin ECOWAS da aka gudanar a Abuja.
Shugaba Bio ya ce ƙungiyoyin ta’addanci na amfani da raunin tsaron iyakoki wajen kai hare-hare tsakanin ƙasashe, yana mai jaddada buƙatar ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro, musayar bayanan sirri da ayyukan soji a tsakanin ƙasashen mambobi.
A wani ɓangare kuma, ECOWAS ta naɗa Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, a matsayin Shugaban farko na Majalisar Kasuwancin ECOWAS, domin ƙarfafa rawar ɓangaren masu zaman kansu a ci gaban tattalin arzikin yankin.


