Ƙungiyar Gwamnonin jihohin arewa ta Naɗa Ezekiel Gomos a matsayin babban darakta don karfafa haɗin kan yankin
Kungiyar gwamnonin jihohin Arewa (NSGF) ƙarƙashin jagorancin Shugabanta kuma Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ta amince da naɗin Mista Ezekiel Gomos, OFR, a matsayin Babban daraktan sakatariyar ƙungiyar.
Naɗin dai ya yi daidai da sabbin alƙawuran da ƙungiyar ta ɗauka na ƙarfafa ayyukan hukumominta da inganta haɗin kai a tsakanin jihohin Arewa 19 wajen tinkarar ƙalubalen da yankin ke fuskanta.
A cewar ƙungiyar, samar da ofishin Babban Daraktan wani kyakkyawan mataki ne na mayar da Sakatariyar ya zuwa cibiya mai inganci wajen haɗa kai da inganta manufofi, da aiki tare da kuma samar da tsare-tsaren ci gaba na dogon zango.
Mista Gomos, wadda tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Filato ne, ƙwararre ne a fannin tattalin arziƙi, siyasa da aikin gwamnati, da kuma inganta harkokin mulki, da bunƙasa kamfanoni masu zaman kansu da kuma ciyar da jama’a gaba.
Ƙwarewarsa ta haɗa da manyan ayyuka a manyan cibiyoyi masu tasiri irin su New Nigeria Development Company (NNDC) da kuma Hukumar Shirya Jarrabawa ta Yammacin Afirka (WAEC).
Bugu da ƙari, ya kasance ƙwararren mai bada shawara kuma shugaban tsangaya a Makarantar Kasuwanci ta Jos (JBS), makarantar data mayar da hankali wajen bunƙasa harkokin kasuwanci, horas da shugabanni da tsare-tsaren manufofi.
Mista Gomos ya shafe kusan shekaru ashirin yana aiki a Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabaru ta Kasa (NIPSS) dake Kuru, inda ya bada gudummawa wajen horar da manyan shugabanni a faɗin Najeriya ta fuskar manufofi, dabaru da ci gaban ƙasa.
Sauran harkokin karatu na sabon Babban Daraktan sun haɗa da digiri na ɗaya dana biyu da ya yi a jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya da kuma Jami’ar East Anglia ta kasar Birtaniya.
Har ila yau mamba ne a wasu manyan cibiyoyi na duniya, ciki har da Hubert Humphrey Fellowship (na Jami’ar Minnesota) da Chevening Scholarship na Birtaniya da kuma kasancewarsa mamba a hukumar ci gaba ta Majalisar Dinkin Duniya (UNDP Fellowship) a Cibiyar Horaswa ta Ƙungiyar Ƙwadago ta Duniya (ILO) a Turin.
Gomos ya halarci manyan horaswar shugabanci a Makarantun Harvard Kennedy, da Jami’ar Chicago Booth School of Business, da Makarantar Kasuwanci ta Jami’ar Durham.
Da yake gabatar da takardar naɗin, Gwamna Inuwa Yahaya ya buƙaci Mista Gomos ya yi amfani da ƙwarewarsa ta fannin jagoranci dabaru, ci gaban cibiyoyi da tsare-tsare don ƙarfafa sakatariyar Ƙungiyar Gwamnonin ta Arewa zuwa wata katafariyar dandalin haɗin gwiwar tsaro da tattalin arziƙin yankin da kuma ci gaba mai ɗorewa a faɗin Arewa.
Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewan ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa naɗin zai haifar da wani sabon yanayi na zurfafa haɗin gwiwa, da ingantaccen haɗin kai da kuma samar da matakan da suka dace da yankin don fuskantar ƙalubalen Arewa.



