Farashin mai ya fadi fiyeda da dala daya, a yau Alhamis, yayinda masu zuba jari suka maida hankali kan kokarin sulhu a yakin Rasha da Ukraine, domiin suna ganin babu wata baraka, da harin da Ukraine ta kai da jiragen Drones kan harkokin mai a Rasha, da kuma kama jirgin dakn mai a gabar ruwan Venezuela.
Zuwa karfe 12 saura agogon Amurka misalin karfe shida sura agogon GMT man fetur da ake kira Brent yayi kasa da kusan maki biyu, watau kamar dala daya da kobo 18 na kudin Amurka. Mai da ake kira Wrst Texas, ya fadi da usan kashi biyu. Yanzu gangar danyen mai na Brent a farashinsa dala 61 da centi uku.


