Farashin man fetur ya tashi ranar Jumu’a, akwai yiwuwar faduwarsa mako na biyu a jere saboda hasashen samar da shi da yawa, da kuma yiwuwar samar da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine, ya kawar da dar-dar din da aka shiga na matsalar da ka iya aukuwa biyo bayan sarkafawa jiragen dakon man Venezuela takunkumi.
Farashin mai a kamfani Brent Crude Futures ya tashi da kobo 52, ko Kashi 0.87 cikin dari, inda ko wacce gangar mai ta tashi kan dala 60.34, yayin da kuma kamfanin West Texas Intermediate Crude ya karu da kobo 51 ko kashi 0.9 cikin dari, inda ko wacce gangar mai ta tashi kan dala 56.66.
Masu bincike na hasashen cewa za’a samu mai me yawa a fadin duniya shekara me zuwa, wanda ya samu bunkasa daga kasashe masu arzikin man fetur na OPEC, da kungiyoyin samar da man, bugu da kari kuma daga Amurka da sauran masu sarrafa shi.


