Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Dokta Nasir Idris, Kauran Gwandu, ya rattaba hannu kan Dokar Kasafin Kuɗi ta shekarar 2026, wadda aka yi wa lakabi da “Kasafin Sauya Fasali da Ƙarfafa Al’umma”, lamarin da ya mayar da kasafin ya zama doka.
An gudanar da bikin sanya hannu a ranar Talata a Fadar Gwamnati da ke Birnin Kebbi, bayan Shugaban Majalisar Dokokin jihar Kebbi, Muhammad Usman Zuru, ya gabatar wa Gwamnan kasafin da Majalisar ta amince da shi.
Kasafin Kuɗin shekarar 2026 ya zo da jimillar kuɗi ₦642,930,818,157.99k, wanda ya haɗa da kuɗaɗen gudanarwa da na manyan ayyuka (recurrent da capital expenditures) domin shekarar kasafin kuɗi ta 2026.
Da yake jawabi, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Alhaji Muhammad Usman Zuru, ya bayyana kasafin a matsayin wani muhimmin tarihi da aka cimma sakamakon kyakkyawar haɗin kai tsakanin ɓangaren zantaswa da na majalisa.
Zuru ya bayyana cewa Majalisar ta yi cikakken nazari, muhawara da tantance kasafin bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulki da ƙa’idojin majalisa, kafin tura shi ga Gwamna domin amincewa.
Ya ƙara da cewa kasafin kuɗin 2026 ya bayyana hangen nesa na Gwamna Nasir Idris wajen samar da ci gaba mai ɗorewa, bunƙasa ababen more rayuwa, haɓaka ɗan Adam da walwalar al’ummar jihar Kebbi baki ɗaya.
Ya kuma jaddada cewa kyakkyawar fahimta tsakanin ɓangarorin biyu ta sanya jihar Kebbi ta zama abin koyi wajen kula da kuɗin gwamnati da shugabanci nagari.
Shugaban Majalisar ya kuma bayyana cewa cikin shekaru biyu kacal a wannan gwamnati, Majalisa ta 10 ta amince da dokoki 60, dukkaninsu kuma sun samu rattaba hannun Gwamna wani abin alfahari da ba a taɓa samun irinsa ba, wanda ke nuna girmamawar Gwamna ga dimokuraɗiyya da jajircewarsa wajen aiwatar da sauye-sauye.
Ya tabbatar da cikakken goyon bayan Majalisar ga manufofin ci gaban gwamnatin.
A nasa jawabin, Gwamna Nasir Idris ya nuna matuƙar godiya ga Shugaban Majalisar, da shugabannin majalisa da dukkan mambobinta bisa jajircewa, kishin ƙasa da mayar da hankali kan muradun al’umma wajen yin dokoki.
Gwamnan ya bayyana Majalisar a matsayin “Gidan Gaskiya na Al’umma”, yana mai cewa tsauraran matakan da Majalisar ke ɗauka wajen duba shawarwarin gwamnati na ƙara inganta shugabanci tare da tabbatar da cewa dokoki da manufofi sun dace da muradun al’ummar Jihar Kebbi.
Ya jaddada cewa gwamnatinsa ta yi aiki cikin cikakkiyar fahimta da Majalisa ba tare da rikici ba, yana mai cewa shugabanci haɗin kai ne, ba fafatawa ba, domin hidimar al’umma gaba ɗaya.

Gwamna Idris ya kuma nuna muhimmancin ƙara hanyoyin tara kuɗaɗen shiga na cikin gida (IGR), yana mai cewa nasarar aiwatar da kasafin 2026 na dogaro da inganta kudaden Shiga domin ƙara wa tallafin tarayya, wanda bai wadatar da bukatun ci gaban jihar ba.
Ya tabbatar da cewa kasafin ya fi ba da fifiko ga ayyukan da suka shafi al’umma kai tsaye, ƙarfafa matasa, bunƙasa ababen more rayuwa da inganta ayyukan gwamnati, tare da yin sassauci a inda ya dace domin samun fa’ida mafi girma ga jama’a.
A ƙarshe, Gwamnan ya jaddada jajircewar gwamnatinsa ga al’ummar Jihar Kebbi, tare da nuna kyakkyawan fata cewa haɗin kai tsakanin ɓangaren zangltaswa, majalisa da shari’a zai ƙara ƙarfi a 2026, wanda zai hanzarta ci gaba da samar da zaman lafiya mai ɗorewa.


