Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Gwamnatin Najeriya Ta Tura Mutane 386 Gidan Yari
Published: April 11, 2026 at 7:28 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin Tarayya ta bayyana samun nasarar daure mutum 386 daga cikin mutum 508 da ake tuhuma da laifukan ta’addanci a wata gagarumar shari’ar bai daya da aka gudanar.

Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin kasar , Lateef Fagbemi (SAN), ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai ranar Juma’a. Ya bayyana cewa, Adadin Wadanda Aka Daure Mutum 386, Wadanda Aka Wanke Mutum biyu (2), Sai Wadanda Aka Sallama Mutum takwas (8).

Sauran Wadanda Ba a Kammala Nasu Ba Mutum 112, za a ci gaba da shari’arsu daga ranar 15 zuwa 18 ga watan Yuni.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa an fara wannan shari’ar ce tun ranar Talata a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja. Wadanda aka samu da laifin an yanke musu hukuncin zaman gidan yari daban-daban, kama daga shekara takwas (8) har zuwa daurin rai-da-rai, dangane da nauyin laifin da kowannensu ya aikata.

Fagbemi ya jaddada cewa wannan hukunci wani sako ne ga masu aikata manyan laifuka cewa Najeriya ba za ta amince da ta’addanci ba. Ya kuma jinjina wa alkalai 10 da suka sadaukar da hutunsu na Ista domin gudanar da wannan shari’a ta musamman.

Domin tabbatar da adalci da gaskiya, kungiyoyi da dama sun halarci zaman kotun a matsayin masu sanya ido, ciki har da Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA), Hukumar Kare Hakkin Dan-adam ta Kasa, Kungiyar Amnesty International, Da Wasu kungiyoyin farar hula.

Wannan shari’ar tana daya daga cikin matakai na tara (Phase 9) da gwamnati ke dauka domin dakile matsalar tsaro da kuma tabbatar da cewa wadanda aka dade ana tsare da su sun fuskanci shari’a domin maido da zaman lafiya a kasar.

Afrika, Labarai, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Jirgin Hakar Mai Daga Turkiyya Ya Isa Mugadishu

Karin Labarai Masu Alaka

Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya Tayi Kakkausar Lafazi Game Da Harin Maiduguri Afrika
Harin Makami Mai Linzami Da Rasha Ta Kai Yayi Barna Sosai A Ukraine Afrika
Kasar Faransa Zata Bunkasa Nukiliyarta Afrika
Shugaban Amurka Yayi Watsi Da Tattaunawar Kawo Karshen Yaki Da Iran Afrika
An Gudanar Da Addu’oi Ga Mutane 16 Da ‘Yan Bindiga Suka Kashe a Australiya Tsaro
An Garkame Wani Babban Soja A Kasar Australiya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Gwamnatin Najeriya Ta Tura Mutane 386 Gidan Yari
  • Jirgin Hakar Mai Daga Turkiyya Ya Isa Mugadishu
  • Farashin Mai Ya Doshi Dala 100 Kowacce Ganga
  • Shugaban Lebanon Ya Nemi Gudanar Da Shawarwari Kai Tsaye
  • Mataimakin Shugaban Amurka Ya Sauka A Islamabad Domin Tattaunawa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaba Saied Yana Cigaba Da Samun Goyon Bayan Al’ummar Kasar Tunisiya Afrika
  • China Ta Kori Wakilan Majalisar Dokoki Uku A Kasar Labarai
  • Gwamna Fubara Ya Koma Jam’iyar APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Limamin Da Ya Ceci Kiristoci Lokacin Rikicin Addini A Jihar Filato Ya Rasu Labarai
  • Farashin Mai Ya Cigaba Da Tashi Afrika
  • Margayi Shugaba Muhammadu Buhari 1942-2025 Labarai
  • Trump Yayi Kira Ga ‘Yan Ƙasar Iran Su Ci Gaba Da Zanga Zanga Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Isra’ila Zata Mamaye Lebanon Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.