Gwamnatin Tarayyar Najeriya tana neman aron Naira Triliyan N17.89 domin ɗaukar nauyin kasafin kuɗin 2026
Gwamnatin Tarayya na shirin kara yawan bashin da take karbowa zuwa Naira Triliyan N17.89 a shekarar 2026 domin cike gibin kasafin kuɗi da ke karuwa, kamar yadda sabon tsarin kasafin kudin 2026 ya nuna.
Sabon bayanin kasafi daga Ma’aikatar Tsare-tsaren Kasafi ya nuna cewa sabbin bashin da gwamnati za ta ci za su tashi daga Naira Triliyan N10.42 a 2025 zuwa Naira Triliyan N17.89 a 2026, karin da ya kai Naira Triliyan N7.46 (72%) cikin shekara guda.
An kiyasta gibin kasafin 2026 zai kai Naira Triliyan N20.12, sama da Naira Triliyan N14.10 da aka amince da shi a 2025 karin 43%. Duk da haka, yawan gibin idan aka kwatanta da kudaden cinikayya na cikin gida GDP zai ragu zuwa kashi 3.61% saboda karin hasashen GDP.
Kudin shiga kuma na raguwa sosai daga Naira Triliyan N38.02 a (2025) zuwa Naira Triliyan N29.35 a (2026), raguwar da ta kai kashi 23% hakan na nuna cewa gwamnati na dogaro sosai da karban bashi.


