Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan 42 don kula da lafiyar ‘yan Najeriya miliyan 10 masu ƙaramin ƙarfi a 2026.
Gwamnatin Tarayya ta gabatar da kudirin ware Naira biliyan 42.18 domin samar da muhimman ayyukan kiwon lafiya ga ‘yan Najeriya miliyan 10 da ake ganin suna cikin masu rauni, a cikin kasafin kudin shekarar 2026 da aka gabatar wa Majalisar Tarayya.
Wannan kudin na daga cikin jimillar Naira tiriliyan 2.48 da aka ware wa bangaren kiwon lafiya a kasafin kudin shekarar, inda aka tanadi kudaden domin sayen magunguna, kayan amfani a asibitoci, kayayyakin aikin likitanci, sinadaran gwaje-gwaje da kayan gwajin cututtuka, da nufin inganta samun kulawar lafiya musamman ga talakawa a fadin kasar.
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya mika kudirin kasafin kudin shekarar 2026 ga majalisar Dokoki ta Kasa a watan da ya gabata, inda ya bayyana muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta bawa fifiko a daidai lokacin da kasar ke fuskantar kalubalen tattalin arziki da zamantakewa.
A cewar bayanan kasafin kudin, bangaren tsaro da kariya ne ya samu kaso mafi tsoka da Naira tiriliyan 5.4, sai bangaren gine-ginen ababen more rayuwa da Naira tiriliyan 3.56, ilimi da Naira tiriliyan 3.52, sannan kiwon lafiya da Naira tiriliyan 2.48, wanda ya zama bangare na hudu mafi girma a jerin fifikon kashe kudin gwamnati.
Daga cikin jimillar kasafin kudin Tarayya na Naira tiriliyan 58.47, kudin da aka ware wa kiwon lafiya ya kai kusan kashi 4.2 cikin 100. Wannan kasafin ya kunshi shirye-shirye daban-daban na rigakafin cututtuka, samar da ayyukan lafiya, sayen kayan aikin asibiti, da tallafa wa rukunin al’umma masu rauni.
A jawabinsa yayin gabatar da kasafin kudin, Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin bangarorin kiwon lafiya da ilimi wajen gina jari na bil’adama, yana mai cewa babu wata kasa da za ta ci gaba fiye da ingancin mutanenta.
Shugaban kasar ya kuma bayyana rawar da abokan hulda na kasa da kasa ke takawa wajen tallafa wa tsarin kiwon lafiyar Najeriya, inda ya ce tattaunawa da gwamnatin Amurka ta samar da damar samun tallafin fiye da dala miliyan 500 domin aiwatar da muhimman shirye-shiryen lafiya a kasar.


