Gwannatin Jihar Kebbi ta Arawa Maniyyata Kuɗin Aikin Hajji wanda zasu biya cikin kwana goma.
Da yake gabatar da jawabi a Ofishin shi na Hukumar Jin Daɗin Alhazzai ta Jihar Kebbi, Shugaban Hukumar, Alh Faruk Aliyu Yaro (Jagaban Gwandu) ya bayyanawa manema labarai cewa Gwannatin Jihar Kebbi ƙarƙashin jagorancin Mai girma Gwamna Comr Dr Nasir Idris (Kauran Gwandu) ta bada aron kuɗi na Naira Biliyan goma (₦10B) don sauƙaƙawa Maniyyata domin su biya kudin cikin kwana goma wato ranar 16 ga watan 12 2025.
Kazalika, Alh Faruk ya ƙara da cewa jirgin Fynas, ne zai yi jigilar Alhazzan Jihar Kebbi inda za’a fara a ranar 3 ga watan 5 2026, kuma Jirgin shine Jirgin da yayi jigilar Mahajjatan Jihar Kebbi a shekarun 2024, 2025 da 2026 in sha’Allah.
Don haka ake kira ga Maniyyata da su biya kudin su nan da kwana 10 wanda shine maƙasudin aron kuɗin da Gwamnatin jihar Kebbi tayi don a ƙara samun damar Maniyyata daga Jihar Kebbi.


