Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC) ta rufe wani gida da ke da alaka da tsohon Antoni Janar na ƙasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, a daren Laraba, a matsayin wani bangare na binciken cin hanci da rashawa da ake yi masa.
Rahotanni sun ce jami’an EFCC tare da jami’an tsaro sun isa gidan, inda aka ce Nana Hadiza Buhari, ’yar tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kuma matar Malami, tana nan a lokacin da aka gudanar da aikin.
Matakin na zuwa ne yayin da EFCC ke ci gaba da tsare Malami bisa zargin cin hanci da rashawa, halasta kudaden haram da wasu laifuka da suka shafi kudaden Abacha da aka kwato.
EFCC ta bayyana cewa belin da aka ba Malami a baya an soke shi saboda rashin cika sharudda, kuma har yanzu yana hannun hukuma domin ci gaba da bincike.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wata sanarwa daga bangaren Malami ko iyalan Buhari kan lamarin.


