Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Hukumar Tsaron Teku A Libya Tafara Janye Jirgi Mai Dauke Da Iskar Gas
Published: March 26, 2026 at 10:09 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar tsaron gabar tekun Libya ta fara jan wani jirgin ruwa mai ɗauke da iskar gas mai narkewa (LNG) da ya lalace, wanda ƙasashen yankin Bahar Rum da dama suka yi gargadin cewa na iya haifar da haɗarin muhalli, bayan ya yi makonni yana yawo ba tare da matuƙa ba, kamar yadda Gwamnatin Haɗin Kan Ƙasa da ke Tripoli (GNU) ta bayyana.

Jirgin mai ɗauke da tutar Rasha mai suna Arctic Metagaz, wanda ke ɗauke da iskar LNG daga tashar Murmansk ta yankin Arctic, ya kasance yana yawo tun farkon watan Maris, lokacin da Ma’aikatar Sufuri ta Rasha ta ce jiragen ruwa marasa matuƙa na Ukraine sun kai masa hari.

Ba tare da ma’aikata a cikinsa ba, daga ƙarshe jirgin ya kusanto gabar tashar jiragen ruwa ta Zuwara da ke yammacin Libya.

Ƙasashen Italy, France, Spain da wasu ƙasashe shida (6) na kudancin Tarayyar Turai sun aika wasiƙa ga Hukumar Tarayyar Turai a makon da ya gabata, suna gargadin cewa jirgin na haifar da “barazana ta gaggawa kuma mai tsanani ga wani babban bala’in muhalli.”

Ministan Sufuri na gwamnatin GNU, Mohamed Al-Shahoubi, ya ce a cikin wani saƙon bidiyo cewa an ɗora wa Hukumar Mai ta Ƙasa a Libya alhakin sauke kayan da ke cikin jirgin na Rasha. Ya ƙara da cewa ana haɗa kai ta hannun Ma’aikatar Harkokin Waje da hukumomin Rasha da Malta domin ɗaukar matakan tabbatar da tsaron zirga-zirgar ruwa a yankin Bahar Rum.

Labarai, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Rasha Ta Yiwa Amurka Tayin Daina Bada Bayanan Sirri
Next Post: Kasar India Ta Sayi Iskar Gas Daga Iran

Karin Labarai Masu Alaka

Hamas Ta Kwance Damara Afrika
Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi Afrika
Sallah Sai Ranar Juma’a A Najeriya: Fadar Sarkin Musulmi Afrika
Amurka Tafara Yiwa Kasar Iraq Barazana Amurka
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha: Tura Sojojin Birtaniya Ukraine Zai Kara Ta’azzara Yaki Labarai
Takaddama Ta Barke Tsakanin Lebanon Da Isra’ila Akan Bakin Iyaka Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kasar Sham Ta Sanar Da Tsagaita Wuta Tsakaninta Da Kungiyar Kurdawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Trump Yayi Kira Ga ‘Yan Ƙasar Iran Su Ci Gaba Da Zanga Zanga Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Sakataren Gwamnatin Amurka Ya Bayyana Bawa Kungiyoyin Agaji Damar Kai Taimako Sudan Amurka
  • China Ta Yi Kira Da Kasashen Gabas Ta Tsakiya Su Hada Kai Labarai
  • Baba Buhari Yayi Zargin Ansaka Masa Na’urar Tsaro Labarai
  • Majalisar Dokokin Rivers Zata Tsige Fubara Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Nuhu Ribadu Ya Mika Dalibai 100 da Aka Ceto Ga Gwamnatin Jihar Neja Labarai
  • Amurka Na Gargadin Rwanda Da Ta Mutunta Alkawali Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.