Ministan harkokin wajen China yace hukumomi a birnin Beijing su na jaddada goyon bayansu ga kasar Somaliya wajen karewa da tabbatar da ikon ta, da kuma dukkan yankunanta.
Wata sanarwar ma’aikatar harkokin wajen China ta ce Wang Yi, ya furta wannan a tattaunawar da yayi ta wayar tarho da takwaransa na Somaliya, a lokacin rangadin da yake yi a Afirka, inda ya kara da cewa China tana adawa da hada kan da yankin Somaliland mai neman ballewa daga Somaliya yake yi da hukumomi a Taiwan mai neman raba kanta daga China.
Tun da farko an shirya ministan harkokin wajen na China zai ziyarci Somaliya a bangaren rangadin sabuwar shekara da ya kai Afirka, wadda ta kunshi kasashen Habasha, Tanzaniya da Lesotho amma kuma daga baya an jinkirta ziyara zuwa Somaliya a saboda abinda ofishin jakadancin China ya bayyana a zaman sauya tsarin rangadin.


