Iran ta sanar da cewar duniya ta shirya don kuwa farashin gangar danyen mai daya sai ta kai dalar Amurka $200 a dai-dai lokacin da dakarunta suka kai hari kan jiragen ruwa na kasuwanci a ranar Laraba a tekun Gulf da aka katange.
Har ila yau Iran ta yi luguden wuta kan Isra’ila da wasu yankuna a Gabas ta Tsakiya duk a yau, abin da ke nuna cewa har yanzu za ta iya fafatawa duk da abin da ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta bayyana a matsayin hari mafi muni da Amurka da Isra’ila suka kai.
Farashin man fetur da ya tashi a farkon makon nan ya samu sauki kuma kasuwannin hada-hadar hannayen jari sun farfado, inda masu zuba jari ke yin caca a yanzu cewa shugaban Amurka Donald Trump zai yi gaggawar kawo karshen yakin da ya fara tare da Isra’ila kusan makonni biyu da suka gabata.
Trump, wanda ya yi ta kokarin tabbatar wa kasuwanni a wannan makon cewa za a kawo karshen yakin nan ba da dadewa ba, ya shaida wa Axios a wata hira ta wayar tarho cewa “a zahiri babu wani abu da ya rage” da za a kai wa Iran hari. “Kadan wannan da wancan. Duk lokacin da nake son kawo karshensa, zai kare,” in ji Trump yayin wata ‘yar gajeruwar hira ta wayar tarho.


