Iran ta rufe sararin samaniyar ta har sai an bayar da wata sabuwar sanarwa
Iran ta rufe sararin samaniyar ta gaba ɗaya har sai wani sabon umarni, bayan fashe-fashe da dama da suka girgiza babban birnin Tehran da wasu wurare, kamar yadda hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta ƙasar ta bayyana.
“Kasar Iran ta rufe sararin samaniyar ta gaba ɗaya har sai an bayar da wata sabuwar sanarwa,” in ji kakakin Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Iran, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Tasnim News Agency ya ruwaito.


