Mutane a kasar Iran sun fito don nuna goyon baya ga sabon shugaban Addini Ayatollah Mojtaba Khameni a ranar Litinin, wanda dora shi a kan mukamin ya sa aka cire rai da kawo karshen yakin na gabas ta tsakiya nan da nan, abinda ya jawo hargitsewar kasuwannin duniya.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce bai yarda da zaben Mojtaba Khameni mai shekaru 56 a duniya ba, kuma ya bukaci Iran tayi saranda kai tsaye.
Gidan talabijin na Iran ya nuna taron mutane da yawa a birane da dama sun fito nuna goyon bayan su ga sabon shugaban, inda suke dauke da tutar kasar da kuma hoton mahaifin shi, wanda ya rasu sakamakon harin Amurka da Isra’ila.


