Jagoran adawa na jam’iyyar Labour Party (LP) Mr. Peter Obi, wanda kuma ya zamo mutum na uku a zaben da aka gudanar a 2023. Ya amsa gayyatar tafiyar jam’iyyar adawa ta ADC, inda ya isa jam’iyar don ayyana makomar siyasar shi.
Haka zalika jam’iyyar ta ADC duk a yau ta karbi sanata Ben Ndi Obi, kuma wanda ya taba yiwa jam’iyyar ACN takarar mataimakin shugaban kasa a shekarar 2007, ya bar jam’iyyar shi ta PDP don shiga jam’iyyar ADC.

Kana Sanata Enyinnaya Abaribe mai wakiltar Abia ta kudu, dan jam’iyyar APGA, ya bar ta don shiga jam’iyyar ADC.
Farfesa Muhammad Sani Yahaya, wanda ya yayi takarar Gwamnan jihar Taraba a zaben 2023, ya canza sheka daga jam’iyyar tasa zuwa abbabr jam’iyyar hamayyata ADC.

Duk a yau din dai wasu ‘yan majalisun tarayya biyar daga jihar Anambra sun fice daga jam’iyyar tasu tare da jagoran nasu don shiga ADC, wadanda suka hada da
– Hon. Uchenna Harris
– Hon. Emeka Idu Godwin
– Hon. Ozodinobi George
– Hon. Ogene Victor Afamefuna
– Hon. Lilian Obiageli Orogbu


