Rasha da Ukraine suna zargin juna da auna hare hare kan farar hula a ranar farko ta sabuwar shekara, inda Rasha tayi zargin Ukraine ta kai mummunar hari akan wai O’tel a yankin kudancin kasar data mamaye, yayin da hukumomi a Kyivi suke zargin Rasha ta auna hare hare kan tashoshin makamashin wutan lantarki.
Rahotannin nan suna zuwa ne a dai dai lokacin da aka zafafa yin shawarwari da zummar kawo karshen yakin na kusan shekaru hudu, ko wacce daga cikin kasashen biyu masu gaba da juna, tana zargin dayar da kokarin cewa ra’ayinta ne ya fi samun karbuwa da goyon bayan shugaban Amurka.
“A ranar sabuwar shekara, da-gangan Rasha ta auna Ukraine da hare hare da jiragen drones da basu da matuka cikin dare.”
Shugaba Volodymyr Zelensky ya rubuta a shafin sa dake dandalin Telegram, yana mai cewa a hare haren, Rasha ta auna tashoshin samar da wutan lantarki a yankunan kasar bakwai.
A nata bangaren Rasha ta zargi Ukraine cewa ta kashe akalla mutane 24 ciki har da jariri a wani hari data kai da jiragen drones kan wani O’tel da wurn cin abinci da shakatawa a yayinda mutane suke murnar shigar sabuwar shekara a yankin Ukraine na Kherson dake kudancin kasar.
Sai dai da take magana, rundunar mayakan Ukraine wacce ta sha sukar Rasha a kan kai hare hare kan farar hula, tace hare haren da take kaiwa duka tana auna su ne kan cibiyoyin soja da kuma tashoshin makamashi, amma bata ce komi ba kan zargin kai hari kan O’tel ba.
Shugaba Zelensky yace, harin na Rasha yayinda ake hutun sabuwar shekara, ya nuna cewa Ukraine ba zata iya jurewa jinkiri kan kayan tsaro ta sararin samaniya ba.


