Rundunar sojojin kasar Sham ta ce yau alhamis zata bude hanya domin fararen hula su fice daga wani yanki na lardin Aleppo da ake kara jibga sojoji cikinsa, a bayan kazamin fada da aka gwabza tsakanin dakarun na gwamnati da na Kurdawan cikin birnin Aleppo.
Wannan sanarwa da rundunar sojojin ta fitar cikin daren laraba, wadda ta ce fararen hula na iya ficewa ta hanyar da za a bude daga karfe 9 na safiya zuwa 5 na yamma agogon kasar, tana nuna alamun cewa ana shirin kai farmaki a garuruwan Dar Hafer da Maskana da yankunan dake kewaye da nan, masu tazarar kilomita 60 a gabas da birnin Aleppo.
Rundunar sojojin ta yi kira ga dakarun kungiyar SDF dake karkashin jagorancin Kurdawa da ta janye mayakanta zuwa tsallaken kogin al-Furat, wato zuwa gabas da inda ake takaddama a kai.
Tuni dai rundunar sojojin Sham ta tura karin dakaru zuwa yankin, a bayan da ta ce kungiyar SDF ma tana ta kara jibge sojojinta a wurin.
Gwamnati ta zargi kungiyar SDF da laifin kai hare-hare da jiragen drone na birnin Aleppo, ciki har da wani hari kan ginin gwamnatin lardin Aleppo jim kadan a bayan da wasu ministoci biyu suka yi hira da ‘yan jarida.


