Wasu kwararru kan harkokin tsaro a Amurka sun ce tayin da kasar Ukraine ta yi na yin watsi da burin neman shiga cikin kungiyar kawancen tsaro ta NATO, bai kai wanda zai iya canja akalar tattaunawar neman sulhun da ake yi yanzu ba.
A lokacin tattaunawa da wakilan Amurka ranar lahadi a kan shirin sulhu tsakanin Rasha da Ukraine, shugaba Volodymyr Zeklensky yayi tayin watsar da yunkurin da kasarsa ke yi na neman shiga kungiyar kawancen tsaro ta NATO.
Shugaban yace maimakon neman shiga NATO, kasar zata nemi tabbacin na tsaro, watau kariya daga Amurka da kasashen Turai da wasunsu.
Daraktan nazarin tsaro da manufofin hulda da kasashen waje cibiyar nan ta CATO institute, Justin Logan, yace wannan tayin ba zai canja komai a tattaunawar neman sulhun da ake yi ba, yana mai fadin cewa wannan wani yunkuri ne kawai da Ukraine keyi na neman nuna cewa tana son a yi sulhu.
Logan da wani farfesa na nazarin muhimman muradu na kasa a Jami’ar Florida, Andrew Michta, sun ce da ma zai yi wuya ga Ukraine ta samu shiga kungiyar ta NATO, saboda haka wannan ba wani muhimmin batu ba ne a yanzu.
Sai dai kuma, ba kowa ne yayi watsi da tayin na Zelensky ba amma wani tsohon mai bada shawara kan hulda da kasashen waje a gwamnatin shugaba Obama , Brett Bruen, yace wannan sassauci da Ukraine ta yi babba ne kuma yana da muhimmanci, domin kuwa Zelensky yana nuna ma duniya cewa shi mai neman zaman lafiya ne، yayin da har yanzu babu wani abu guda da kasar Rasha ta nuna sassauci a kai daga cikin bukatunta.


