A karon farko, kudaden shiga da ake samu daga wasu ma’adanai ya zarce na diamond a Namibia, a cewar sashen hakar ma’adanai ta kasar, a inda hauhawar farashin gwal da na uranium suka kara ingiza kudaden da ake samu.
A da diamond ke bada babbar gudummawa wajen cika asusun kasar da kudi, inda ya kai kashi 30 cikin dari na kudaden da ake samu daga kayan da ake fitarwa. Amma kamfanin na daimond ya fuskanci raguwar farashi tun tsakiyar shekara 2022, yawanci saboda karbuwar da duwatsun ado da ake kerawa da injina suka samu.
Kudaden haraji da ake samu daga diamond a wata shida zuwa watan Satumba, ya fadi da kashi 79 cikin 100, bayan da ya fadi da kashi 49 cikin 100 a shekarar da ta gabata, a cewar ma’aikatar Amsar haraji ta kasar.


