Abuja- Jami’ar kula da dakin yara ta babban asibitin Maraba a jihar Nasarawa NAS Rita Danjuma ta ce yaran talakawa wato jarirai na shiga wani hali in rashin lafiya ya same su don rashin kudin saya mu su magani.
Likitar ta ce wani lokacin duk kokarin da su ke yi lamarin ya kan gagara don rashin samun abubuwan da a ke nema don taimakawa yaran kasancewar iyayen yaran ba su da wadatar kudi.
Rita Danjuma da ke magana lokacin da wata kumgiyar jinkai KHADIJA ENTERTAINMENT ta kai kayan tallafi dakin yaran; ta ce ya na da kyau duk masu dan sukuni su rika ziyartar asibitoci don ganin abun da za su tabuka.
Wannan ma kokarin na yiwuwa ne daidai gwargwado a asibitocin gwamnati da talakawa ke iya zuwa jinya “sai dai mu na iyakacin kokarinmu sai mu ba su shawara a kan a samu a nema sai ka ga wani lokaci ma da shi ke ba kudi sai ka ga wani har mutuwa ya na kai wa saboda ba magani ba wani abu da za mu yi don magani da an dan samu an saya ba zai iya kai su ba, wadansunsu har ya na kai ga mutuwa. Kar a manta a zo a na dan lekawa a na taimakawa wadanda ba su da hannu da shuni da za su iya tamakawa kan su.”
Mun ci karo da wani magidanci mai suna Alhassan Abdullahi da ya kawo matarsa don a yi ma ta aikin tiyatar gaggawa amma rashin kudi ya sa shi rikicewa a harabar asibitin don an ba shi adadin kudi Naira 55,000 da kuma kudin magani Naira 20,000 inda ya samu ya sayo magani na Naira 10,000 ya saura da Naira 10 kacal a aljihunsa.
Hajiya Adama Mai Agogo da ta kawo tallafin ta ce ba sai mai hannu da shuni kadai zai iya taimakawa ba “an ce ka gayyaci mai zuciya buki ba mai kudi ba.”
Kan hanyar fita daga asibitin mai gadi Sulaiman Abdullahi ya sanar da mu cewa akwai wani bawan Allah da wasu abokan sa su ka kawo amma yayin da likita ke rubuta maganin da za a sayo sai su ka faki ido su ka gudu inda shi kuma ya riga mu gidan gaskiya bayan ‘yan makonni.
Hakika mutane na zuwa asibiti kullum tamkar yanda su ke shiga kasuwa don sai da lafiya a ke yin motsi da ya fi labewa.


