Kungiyar Ƴan Jarida ta Najeriya ta sake tabbatar da aniyyarta na kare haƙƙin ’yan jarida da inganta walwalar su, yayin da ta bayyana nasarorin da ta cimma tare da sabbin shirye shiryen da take kaddamarwa a taron shugabannin yankin Arewa maso Gabas da aka gudanar a Yola, Jihar Adamawa.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Kwamared Alhassan Yahaya Abdullahi, ya bayyana wannan kuduri a taron da aka yi a cibiyar NUJ ta Yola, inda ya jaddada bukatar haɗin kai domin farfaɗo da ƙarfinsu na ƙungiya a wannan lokaci da ake yawan samun barazana, tsangwama da cin zarafi ga ’yan jarida a sassa daban daban na ƙasar.
Kwamared Alhassan Yahaya Abdullahi ya bayyana cewa shirin ƙungiyar na inganta walwalar membobin ta ya haɗa da ƙaddamar da inshorar rayuwa da inshorar lafiya ga dukkan ’yan jarida masu aiki, yana mai nuna damuwa da cewa a halin yanzu, ƙasa da kashi ɗaya cikin ɗari na ’yan jarida ne ke da inshora.
Yace tsarin inshorar lafiyar zai yi daidai da sabon tsarin ƙasa domin rage nauyin kuɗin magani da suke biya daga aljihun su.
Ya ƙara da cewa ƙungiyar na ƙoƙarin ganin an inganta albashin ’yan jarida ta hanyar rubutawa da mika kudirin dokar Media Enhancement Bill ga Majalisar Dokoki ta tarayya domin a duba shi tare da amincewa.
Shugaban ya yi kira ga Gwamnan jihar Adamawa da ya tallafa wa ƙungiyar ta hanyar samar da sabuwar Mota kirar bas da kuma sake fasalin sakatariyar NUJ ta jihar domin inganta ayyukan ’yan jarida da jin daɗin su.
Ya kuma bayyana cewa ƙungiyar ta samu nasarar sakin ɗan jarida, Mista Matthew Ojo, wanda aka tsare a Jamhuriyar Benin, ta hanyar haɗin kai da jakadancin kasa da jami’an Najeriya.
Wannan, a cewar sa, wani babban misali ne da ke nuna yadda NUJ ke tsaya wa ’yan jarida, ko da kuwa ba cikakken mamba ba ne.


