Majalisar Dattawa ta amince da Janar Christopher Musa a matsayin Ministan Tsaron Najeriya.
A wata sanarwa Mr. Bayo Onanuga ya bayyana cewa, Majalisar Dattawa ta tabbatar da tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, a matsayin Ministan Tsaron kasar.
Majalisar ta amince da nadin Musa ne a ranar Laraba bayan wani tsauraran zaman tantancewa da ‘yan majalisa suka yi, inda suka yi masa jerin tambayoyi masu yawa.
Musa, wanda ya yi ritaya kusan kwanaki 40 da suka gabata, Shugaba Bola Tinubu ne ya nada shi a ranar Talata a matsayin Ministan tsaro inda aika sunansa zuwa Majalisar Dattawa domin tantancewa tare kuma tabbatarwa.


