Ministan kudin Bostwana, ya ce ranar Jumu’a, gwamnatin kasarta yi hasashen tattalin arzikin ta zai yi kasa da kashi kusan 1 cikin 100 a wannan shekarar, saboda sashen ta na ma’adanin diamond na ci gaba da fuskantar kalubale, yayin da yake gabatar da tantance kasafin kudi.
A lokacin da aka gabatar da kasafin kudin a watan Fabrairu, kasar da ke yankin kudancin Afirka ta sa ran samun karin kashi 3.3 cikin dari a ma’aunin tattalin arzikin ta, wato GDP, a wannan shekarar, inda zai farfado da ragin Kashi 3 cikin dari da aka samu a bara.
Amma, har zuwa tsakiyar shekara, sai gashi ana hasashen ba wani kari, saboda tasgaro da aka samu a kasuwar ta diamond bai nuna wata alama ta farfadowa ba.


