Ministan tsaron Somalia yace kasar ba zata amince ana wulakanta kasar ba, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya sake zagin kasar dake gabashin Afirka.
Da yake magana a wani gangami ranar talata da aka shirya a Pennsylvania, domin maida hankali kan nasarorn gwamnatinsa ta fuskar tattalin arziki, Shugaba Trump yayi Allah wadai da barin bakin haure daga kasashe matalauta su shigo Amurka.
“Muna ta karpar mutane daga Somali, wurare dake cike da fitina, ko ba hakka ba, ga dottii, da kazanta, da miyagun laifuffuka.”
Ya kara da cewa “Abunda kawai suka fi kwarewa akai shine, kama jiragen ruwa,” yana maganar kan kama jiragen ruwa a gabar tekun Somalia domiin karpar kudiin fansa.
A makon jiya ne shugaba Trump, ya bayyana ‘yan Somalia, a “zaman shara,” yace babu abunda suke yi illa bin junansu suna kashewa.”
Acikin sakon text, da ya aikawa kamfanin dillancin labarai na Reuters, ministan tsaron na Somalia Ahmed Moalli Fiqi, yace Trump ya maida hankalinsa wajen cika alkawarunda yayi wa Amurkawa mai makon bata lokacinsa kan Somalia.
Yayinda yake godewa Amurka kan taimakon da take baiwa Somalia a yaki da take yi da mayakan sakai a kasar masu alaka da kungiyar al-Qeada, yayi watsi da kalaman batanci da Trump yake yi wa kasar. Yace Somaliyawa suna fuskantar kalubale iri daban daban, amma daga karshe sna jajircewa, kuma duk inda ka same su a fadn duniya, su mutane masu aiki tukuru.


