Mutane shida sun rasa rayukansu yayin da wata babbar mota dauke da yashi ta kutsa cikin wani coci a yankin Epe na Jihar Lagos da yammacin Litinin.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:30 na dare a titin Hospital Road, lokacin da motar ke gangarowa zuwa zagaye (roundabout) sai birkinta ya lalace, direban ya rasa iko, motar ta kutsa cikin cocin.
Wasu masu ibada sun jikkata, yayin da jami’an agajin gaggawa na jihar Lagos suka isa wurin domin ceto wadanda suka makale.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa direban motar ya tsere bayan hatsarin.
Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da mutuwar mutane shida, tare da bayyana cewa motar ba ta da rajista.
An kai gawarwakin wadanda suka mutu dakin ajiye gawa, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.


