Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Muna Kira Ga Kasashen Duniya Su Sa Baki Don A Saki Mohamed Bazoum
Published: November 27, 2025 at 11:05 PM | By: Yusuf Aliyu Harande

A Jamhuriyar Nijar ‘yayan hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum sun bayyana damuwa dangane da yadda ake ci gaba da tsare mahaifansu sama da shekaru 2 bayan kifar da shi daga karaga.
A cewarsu dukkan abubuwan da a ke zargin bayansu da shi ba su da tushe saboda haka su ke kiran kasashen duniya su dubi wannan batu.
A yayin da shugaba Mohamed Bazoum da mai dakinsa Hadiza Bazoum ke cika watanni 28 a tsare ne ‘yayansu suka fitar da sanarwar hadin guiwa domin tada duniya daga barci dangane da halin da mahaifansu ke ciki Wanda kuma su kansu ke shafar ra’ayinsu inji su. Hinda Mohamed Bazoum na daga cikin ‘yayan hambararren shugaban kasar ta Nijar.
Mohamed Bazoum wanda ke tsare a fadar shugaban kasa na fuskantar zarge zargen da hukumomi suka ayyana a matsayin cin amanar kasa. sai dai ‘yayansa na ganin Babu wasu hujjojin da ke gaskata laifikan da ake zarginsa da su.
Kawo yanzu ba wata sanarwar gwamnati a game da wannan batun.
A Watan yunin 2024 kotun shara’ar manyan Jami’an gwamnatin Nijar ta cire wa Mohamed Bazoum rigar kariya amma har zuwa wannan lokaci ba a taba gurfanar da shi gabn alkali ba domin yi masa shari’a.
A baya kotun ECOWAS da kungiyoyin kasa da kasa har ma da hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kare hakkin dan adam sun bukaci gwamnatin mulkin sojan Nijar ta sallame shi sai dai wadanan kiraye kiraye ba su samu karbuwa ba.
SANARWAR YAYAN BAZOUM (1)
Afrika

Post navigation

Previous Post: An Bude Gasar Kwallon Kafa Ta Mata A Najeriya NWFL 2025
Next Post: Mutane Da Yawa Ke Mutuwa A Dalilin Shan Magani Ba Bisa Ka’ida Ba

Karin Labarai Masu Alaka

Dubban Mutane Sunyi Zanga-Zanga A Kasar Australia Afrika
Donald Trump Yace Basu Cimma Matsaya Da Benjamin Natanyahu Ba Afrika
Ana Tuhumar Dan Shugaba Robert Magabe Da Kisan Kai Afrika
Dan Ra’ayin Mazan Jiya Leo Brent Zai Kyautata Alakar Afirka Ta Kudu Da Amurka Afrika
Libya Ta Kulla Yarjejeniya Da Kasashen Faransa Da Amurka Afrika
Indiya Da Brazil Sun Kulla Yarjejeniyar Cinikayya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango
  • Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi
  • Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Kasar Ukraine Ta Yabawa Tarayyar Turai Bisa Bata Tallafi Labarai
  • Akwai Nasara A Tattaunawar Da Akeyi Tsakanin Iran Da Amurka Afrika
  • Kotu A Kasar Faransa Ta Daure Lumbala Shekaru 30 Bisa Laifin Cin Zarafi Labarai
  • Real Madrid: Ta Kori Xabi Alonso Bayan Rashin Nasara A Wasan Kofin Sfaniya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Fintiri: Zamu Maida Jihar Adamawa Sabuwar Duniya Labarai
  • ‘Yan Sandan Habasha Sun Kama Dubban Albarusai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ganduje Ya Nisanta Kansa Da Batan Dadiyata Labarai
  • An Yiwa Dokokin Kare Hakkin Yara Rikon Sakainar Kashi Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.