A kalla mutane 15 suka rasa rayukan su a a gabashin Jamhuriyar Demokradiyar Congo a wani harin ‘yan ta’adda da ake zaton nada alaka da ‘yan kungiyar ISIS, a ranar Laraba, a cewar wasu jami’an lardin su hudu.
Harin ya afku wajajen karfe 7 na dare a kauyen Bafkwakoa dake yankin Mambasa, da Lardin Ituri, kusa da garin Niania a cewar jami’ai.
Baptiste Munyapandi, jami’in gwamnati mai gudanarwa na yankin Mambasa, yace zuwa yanzu hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutane 15, ya kara da cewa ana ci gaba da binciko gawawwaki, kuma adadin mamatan zai iya karuwa. Hukumomin lardin sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an samo gawawwakin mutane 20 zuwa yanzu.
Hukumomi sun dora alhakin harin kan dakarun ‘yan tawayen ADF na Uganda, wanda ISIS ke marawa baya.


