Shugaban hukumar Kula da aikin hajji ta ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya tashi daga Najeriya zuwa ƙasar Saudiyya a wata ziyarar aiki.
A cewar sanarwa da mai taimaka masa kan fannin yaɗa labarai, Ahmad Muazu ya fitar, ziyarar na da nufin kammala shirye-shirye na ƙarshe dangane da aikin Hajjin shekarar 2026, bisa ga jadawalin ayyuka da aka amince da shi.
Ma’aikatan ofishin NAHCON na shiyyar Kano ne suka raka shi zuwa filin tashi, ƙarƙashin jagorancin kodinetan shiyya, Malam Umar Kalgo.
Ziyarar ta nuna ƙudirin NAHCON na fara shirye-shirye tun da wuri da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomin Saudiyya domin tabbatar da nasarar aikin Hajji ga al’ummar Najeriya.


